Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada al’adun muslunci cewa, Sayyid Hassan Esmati shugaban karamin ofishin jakadancin Iran a kasar Senegal Sheilh Tirno Madani Tal shugaban Tijjaniya suka dora tubulin gina cibiyar Darul kur’an.
Bayanin ya ci gaba da cewa shugaban karamin ofishin jakadancin na Iran ya ce babbar manufar samar da wanann cibiya dfai ita ce kara farfado da lamarin kur’ani mai tsarki a kasar, kuma za agina wannan cibiya ne a masallacin daya daga cikin manyan malaman addini na tarihi a kasar Shekh Umar Futi.
Ya lara da cewa wanann cibiyar ta Draul kur’ani za ta kara kawo hadin kai a tsakanin al’ummar na wannan kasa mai tarihi na addini da kuma riko da shi.
A nasa bangaren Sheikh Madani ya yaba matuka da irin wannan kakari da jamhuriyar muslunci ta Iran take yi wajen kara yada lamurra da suka shafi kur’ani a kasar, wanda a cewarsa ko shakka babu hakan zai zama wani aiki da al’ummar kasar ba za su manta da shi ba.
An kuma bayar da wasu kwafin kur’ani mai tsarki guda 30 ga shugaban darikar Muridiyyah a kasar wadanda aka buga aIran.
Kasar Senegal dai tana da cibiyoyin kur’ani guda ksan dubu 17, kuma ana tafiyar da su ta hanyoyi na a’ada.
3365705