IQNA

An Fara Gudanar Da Wani Kamfe Na Raba Kur’anai A Kasar Amurka

22:01 - September 22, 2015
Lambar Labari: 3366436
Bangaren kasa da kasa, domin mayar da martini kan dan takarar shugabancin Amurka Ben Carson a shekarar 2016 ta hanyar gudanar da wani kamfe na raba kwafin kur’ani mai tsarki a kasar Amurka.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na babbar cibiyar musulmin kasar Amurka cewa, wannan cibiya mai kare hakkin bil adama ta fara aikin raba kur’ani a kasar.

Rahoton ya ce wannan kamfe ne da nfin kara fito da matsayin addinin muslunci da kma bayyana koyarwar kur’ani ga mutanen da suke da mummunar fahimta kan wannan addinin mai tsarki, wanda yake kira zuwa ga zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsa da sauran addinai.

Wanann cibiya ta dauki nauyin gudanar da wannan aiki ne n araba kur’ani kyauta ga mutanen Amurka domin tabbatar da akidar musulunci ta zaman lafiya.

Nahad Ewad shi ne shugaban cibiyar, ya bayyana cewa wannan shiri ya hada har da wasu daga cikin jami’an Amurka, wadanda su ma an aike musu da nakwafin na kr’ani domin su karanta su ga a bin da ya kunsa.

Ewad ya ce an yada maganganu na karya da zalunci kan addinin muslunci da musulmi da kur’ani a kasar Amurka bisa jahilcin wannan addini, kuma aikin musulmi ne su wayar da kan mutane dangane da wannan lamari.

Ya ce kwafin na kr’ani ya hada matanin larabci cikake, da kuma tarjama a cikin harshen turanci wanda Muhammad Assad ya tarjama, wanda kuma sananne kan tarjamar larabci zuwa turanci.

Kwamitin musulmin Amurka y araba kur’anai da suka kwafi dubu 130 a tsakanin mutanen kasar Amurka.

3366069

Abubuwan Da Ya Shafa: amurka
captcha