IQNA

Azhar Ta Yi Allawadai Da Nuna Zanen Batunci Kan Manzo (SAW) A Danmark

23:51 - September 29, 2015
Lambar Labari: 3374490
Bangaren kasa da kasa, Ahmad Tayyib Sheikhul Azhar ya yi kakakusar suka kan taron da wasu suka yi a birnin Copenhagen na kasar Danmark kan nuna zanen batun a kan manzon Allah (SAW) d akuma tsokanar musulmi.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Ahmad Tayyib babban malamin Azhar a cikin fushi ya yi kakakusar suka kan taron baje kolin da wasu suka yi a birnin Copenhagen na kasar Danmark da ke kyamar muslunci, kan nuna zanezanen batunci ga  manzon Allah (SAW) d akuma tsokanar musulmi na kasar da ma na duniya baki daya.

Ya ci gaba da cewa abin mamamki ne yadda kasashen turai suke bayar da dama domin cin zarafin addinin muslunci da sunan yancin fadar albarkacin baki, alhali kuwa wannan cin zarafin akidar wasu mutanen ne masu yawa  aduniya.

Malamin ya ci gaba da cewa ci gaba da aikata irin wannan mumunan aiki ba abu ne da musulmi za su amince da shi ba, kuma za a ci gaba da daukar matakai na ganin an kalu balance wannan akida takin jinin muslunci ta hanyoyi da suka dace, da kuma na doka.

Wanann dai bas hi ne karon farko da masu kiyayya da addinin muslunci a kasar ta Danmark suke gudanar da irin wadannan taruka na cin zarafin addinin muslunbci ba, domin kuwa tun shekarun da suka gabat sun sha gudanar da irin wannan taro tare da gayyatar wasu masu irin akidarsu domin bata muslunci.

Babbar manufar wadannan mutane dai ita ce tsokanar musulmi, tare da kokarinb bayyana addinin muslunci a matsayin wani addini na tashin hanklai da rashin son zaman lafiya tsakaninsa da sauran addinai.

3374251

Abubuwan Da Ya Shafa: azhar
captcha