IQNA

Rashin Girmama Hurumin Mahajjata Iraniya Zai Fuskanci Martani Mafi Muni

22:41 - October 01, 2015
Lambar Labari: 3377210
Bangaren siyasa, jagoran juyin juya halin muslunci ta Iran ya bayyana cewa, nuna rashin mutunci da rashin sanin ya kamata ga mahajjatan Iraniyawa zai fuskanci martini, idan kuma aka tashi mayar da martanin zai zama mai mni matuka a kan wadanda suka aikata hakan.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na shafin sadarwa na ofishin jagora cewa, a safiyar yau Laraba (30-09-2015) ce Jagoran juyin juya halin Musulunci kuma babban kwamandan dakarun kasar Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya halarci bikin yaye daliban jami’ar jami’an sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke Jami’ar ilimin sojojin ruwa ta Imam Khumaini (r.a) da ke garin Bushehr.



A jawabin da ya gabatar a wajen bikin, Ayatullah Khamenei yayi ishara da hadari mai sosai rai da ya faru a Mina yayin jifar Shaidan inda ya bayyana hakan a matsayin babbar musiba ga al’ummar Iran sakamakon rasa rayukan dubban alhazai musamman daruruwan alhazan kasar Iran. Har ila yau kuma yayin da yake ishara da wajibcin kafa kwamitin binciken abin da ya faru da zai hada kasashen musulmi ciki kuwa har da Iran, Jagoran cewa yayi: Gwamnatin Saudiyya ba ta aikata abin da ya hau kanta dangane da kokarin da ake yi na dawo da gawawwakin wadanda suka rasa rayukansu ba. Ya zuwa yanzu dai Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana kau da kai da kiyaye ladubba na Musulunci da ‘yan’uwantaka a duniyar musulmi. To amma yana da kyau su san cewa komai kashin cin mutumci ga dubban alhazan Iran a Makka da Madina da kuma kin aiwatar da nauyin da ya hau kansu wajen dawo da gawawwakin (alhazan da suka rasu), to kuwa za su fuskanci kakkausar mayar da martani daga wajen Iran.



Haka nan kuma yayin da yake ishara da kisan gillan da aka yi wa alhazai cikin kishirwa a Mina da kuma sanya iyalan da suke cikin shaukin jiran masoyansu su dawo cikin yanayi na juyayi da zaman makoki, Jagoran cewa yayi: Har ya zuwa yanzu ba a riga da an tantance asalin adadin Iraniyawan da suka rasu ba a yayin wannan hadarin ba. Akwai yiyuwar adadin ya karu zuwa daruruwa. Ko shakka babu wannan babbar musiba ce ga al’ummar Iran.



Har ila yau kuma yayin da yake ishara da wasu rahotanni da suke nuni da yiyuwar mutuwar sama da mutane dubu biyar a hadarin na Mina, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewar: A daidai lokacin da Alkur’ani mai girma yake bayyana Dakin Allah a matsayin wajen aminci sannan kuma hajji a matsayin wani waje na aminci. To amma a halin yanzu wajibi ne a yi tambayar cewa: “Shin wannan shi ne amincin?”.



Ayatullah Khamenei ya sake jaddada wajibcin kafa ‘kwamitin bincike’ tare da taimakon kasashen musulmi ciki kuwa har da kasar Iran don binciko hakikanin abin da ya faru, daga nan sai ya ce: Mu dai a halin yanzu ba za mu yi riga malam masallaci wajen yanke hukunci ba. To amma mun yi amanna da cewa gwamnatin Saudiyya ba ta yi abin da ya dace wajen kula da mutanen da suka sami raunuka yayin wannan hadarin ba. Haka suka bar su cikin kishirwa da matsananciyar wahala.



Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi ishara da matsalolin da suka kunno kai wajen debo gawawwakin wadanda suka rasu da dawo da su gida da kuma kokarin da jami’an kasar Iran suke yi a wannan bangaren, inda ya bayyana cewar: A wannan bangaren ma, gwamnatin Saudiyya ba ta sauke nauyin da yake kanta ba, a wasu wajajen ma har cutarwa take yi.



Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Ya zuwa yanzu dai Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta nuna hakuri da kau da kai, kamar yadda kuma ta kiyaye ladubba na Musulunci da kiyaye ‘yan’uwantaka a duniyar musulmi. To amma ya kamata su san cewa, karfin Iran ya dara na da dama. Matukar tana son mayar da martani kan masu cutar da ita, to kuwa ba za su ji ta dadi ba, babu wani wajen da za su iya gwada damtse (da Iran).



Har ila yau kuma yayin da yake jaddada cewar lalle martanin Iran zai zamanto mai kaushin gaske, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: A lokacin kallafaffen yaki na shekaru takwas, manyan kasashen duniya na gabashi da yammaci bugu da kari kan kasashen yankin nan sun goyi baya da kuma taimakon wani lalataccen mutum (Saddam), to amma daga karshe dukkaninsu sun diba kashinsu a hannu. A saboda haka ne sun san Iran da kyau. Idan ma har ba su san ta ba, to yanzu ya kamata su san ta.



Haka nan kuma yayin da yake ishara da kasantuwar dubban alhazan kasar Iran a Makka da Madina, Jagoran ya ja kunnen cewa: Lalle Iran za ta mai da martani ga komai kashin cin mutumcin alhazan Iran, da kuma duk wata gazawar da Saudiyya za ta nuna wajen kula da kiyaye gawawwakin alhazan da suka rasu.



Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran dai ba ma’abociyar zalunci ba ce, amma ba za ta taba amincewa da zaluncin kowa ba. A saboda haka ba za ta taba take hakkin kowane mutum ko wata al’umma ba, musulmi ne ko wadanda ba musulmi ba. To amma matukar wani yayi kokarin take hakkin kasar Iran da al’ummarta, to kuwa zai fuskanci mai da martani mai kaushi. Cikin yardar Allah kuwa akwai karfin mayar da wannan martanin. Don kuwa al’ummar Iran ma’abociyar karfi da tsayin daka ne.



A wani bangare na jawabin nasa, Ayatullah Khamenei ya bayyana ‘karfafaffen imani’, ‘jaruntaka’ da ‘ilimi’ a matsayin abubuwa guda uku masu tsananin muhimmanci wajen kafa wasu dakaru na soji inda ya ce: Matukar aka rasa imani cikin dakarun soji, to kuwa za a fuskanci matsalar rauni. Idan aka rasa jaruntaka, to kuwa a lokacin da sojoji suka fada wani yanayi mai hatsari, ba za su iya aikata aikinsu yadda ya dace ba. Haka nan idan aka rasa ilimi, to kuwa makaman da sojojin suke da su za su dushe a gaban sojojin da suke fada da su.



Jagoran ya bayyana hare-haren da (Saudiyya da kawayenta) suke kai wa gidaje, tituna, kasuwa da wajajen bukukuwan aure a kasar Yemen a matsayin wani misali na rauni da rashin ruhi na jaruntaka cikin sojojin (da suke kai hare-haren). Haka nan kuma yayin da yake ba wa dakarun kasar Iran shawarar karfafa imani da jaruntaka da kuma irin ilimi da masaniyar da suke da ita, Jagoran cewa yayi: A halin yanzu gwamnatin Musulunci (ta Iran) tana bukatar nau’oi daban-daban na kayayyakin yaki, don kuwa a halin yanzu wannan duniyar da take karkashin ikon Shaidanun masu karfi, wata duniya ce mai hatsarin gaske ga mutane masu tsoron Allah. A saboda wajibi ne a koda yaushe a zamanto cikin shiri.



Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana jaruntaka da ruhi na juyin juya hali, tsayin dakan al’umma wajen tinkarar ma’abota girman kai da kin mika musu wuya a matsayin babban dalilin kiyayyar da ‘yan mulkin mallaka ma’abota girman kai suke yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Don haka sai ya ce: Shirin dakarun soji da suka hada da sojoji, dakarun kare juyin juya halin Musulunci, dakarun sa kai da sauran dakaru na kasa, ba wai kawai shiri ne don samun nasara a kan makiya ba, face dai wajibi ne wannan shiri ya zamanto har da shiri na kai bara da koyar da darasi.



Haka nan kuma yayin da yake ishara da barazanar da masu tinkaho da karfi na duniya suke yi wa Iran, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Al’ummar Iran tsawon shekaru arba’in na juyin juya halin Musulunci musamman tsawon shekaru takwas na kallafaffen yaki sun tabbatar da cewa lalle suna da karfi da kuma ikon tsayin daka a gaban masu bakar aniya.



Har ila yau kuma yayin da yake jaddada cewa al’ummar Iran sun tabbatar wa da duniya cewa su din nan ma’abota tsayin daka da basira ne wajen tinkarar ma’abota girman kan duniya, sannan kuma su din nan masu kiyayewa da kuma kare mutumcinsu ne, Jagoran ya bayyana cewar: Tsayin daka wajen  tinkarar ma’abota girman kai, girmama bil’adama da dukkanin al’ummomi ne.



Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: A kullum haka lamarin ya kasance cewa bugun mummuken muminai lamari ne da zai tilasta (wa ma’abota girman kan) ja da baya.



An fara bikin ne da ziyarar da Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kai makabartar shahidai na jami’an inda ya karanta musu fatiha da addu’ar karin matsayi a wajen Allah.



Har ila yau kuma Jagoran ya ba da lambar yabo ga wasu daga cikin daliban da suka nuna bajinta.



Kafin jawabin Jagoran sai dai, sai da babban hafsan hafsosjin sojin kasa na Iran Laftana Janar Ata’ullah Salehi ya gabatar da jawabin barka da zuwa da Jagora da kuma karin bayani kan irin shirin da sojojin suke da shi wajen tinkarar duk wata barazanar da ka iya fuskanto Iran.



Har ila yau shi ma a nasa bangaren Rear Admiral Hakimi, babban kwamandan jami’ar jami’an sojin ruwa ta Imam Khumaini (r.a) da ke garin Bushehr din ya gabatar da rahoto kan irin ayyukan da aka gudanar a jami’ar.



3375738

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha