IQNA

Tunawa da Wadanda Suka Rasu A Mina Yana Gina Ruhinmu Da Karfafata

23:23 - October 02, 2015
Lambar Labari: 3377426
Bangaren kur’ani, tunawa da wadanda suka rasa rayukansu sakamakon abin da ya faru da Muhajirai zuwa ga Allah da suka rasu a wannan tafarki yana kara karfafa zukatanmu.


Mohammad Taghi MirzaJani shugaban cibiyar kula da ayyukan kur’ani mai tsarkia  zantawarsa da Iqna ya bayyana cewa, za mu ci gaba da tunawa da wadanda suka rasa rayukansu wajen gudanar da ibadar ubangiji, muna masu debe kewa da kyawawan ayyukansu.

Ya ci gaba da cewa abin da ya faru babban rashi ne ga dukaknin al’ummar musulmi na duniya baki daya, haka nan kuma rashin mutane na musamman masu hidima ga tafarkin kur’ani mai tsarki da suka hada Mohsen haji Hassani kargar da za a yi janazarsa a Mashhad na daya daga cikin lamurra masu bakanta rai da sosata.

Haka nan kuma ya kara da cewa za a gudanar da irin wannan janaza ga wasu daga cikin makaranta a garin Ahwaz su ne Mohammad said Saidi Zadeh da kuma Fu’ad Mash’ali, wanda za a yi a garin Abadan.

Mirza Jani ya ci gaba da cewa ko shakka babu an yi rashi babba amma kuma hakan ba zai hana a ci gaba da kara azama wajen ci gaba da bin tafarkin da wadannan bayin Allah suka bi ba har suka kai ga wannan matsayi madaukaki.

Ya ce cibiyarsa ta gudanar da dukaknin abin da ya kamata domin tabbatar da cewa an aiwatar da dukaknin shirin da aka tsara dangane da makaranta da suka rasu a Mina a hajin bana.

3374252

Abubuwan Da Ya Shafa: iran
captcha