Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Daily Trust cewa, sarkin Kano Muhammad Sanusi ya bayyana cewa, idan mahukuntan Saudiyyah ba su dauki mataki ba sakamakon abin da ya faru to Najeriya za ta daina yin jifar shaidan a maimakon hakan sai biya.
Ya ce babu yadda za a yi saboda jifar dutse a raba mutane da rayukansu, domin kuwa rashin yin hakan bay a bata aikin hajin bane, jinin mumimin ya fi wannan aikin na jifar shedan, idan mumini zai rasa ransa saboda shi dole ne ya bar shi.
Sarkin ya kara da cewa suna bukatr wurare a kusa da Mina ga alhazansu, idan km aba haka to za su daina zuwa jifar shedan baki daya sai dai alhazansu su biya hadaya kawai, haka nan kuma yayi kakakusar suka kan yadda aka dora alhakin abin da ya faru kan alhazan Afirka da na Najeriya musamman.
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi wanda shine a wannan shekara yace dolene yanzu fa a sawwake ma yan Najeriya wahalan da suke sha wajen jifa da zaman Mina wajen sama musu wuraren zama a kusa da filin jifan kamar yadda ake sama ma larabawa.
Yace irin fifikon da ake nuna ma larabawa akan bakin fata Sam bai kamataba domin hakan ba musulunci bane.
Yace shi kansa jifan ma ai ba farilla bane, mutum zai iya biyanta da hadaya idan baiyiba . saboda haka da irin wahalhalun da mahajjata suke fuskanta ai gwara a San matakin da za'a dauka nan gaba.