IQNA

Wani Dan Kwallon Kasar Birtaniya Na Cikin Makokin mutuwar Mahaifiyarsa A Mina

20:38 - October 07, 2015
Lambar Labari: 3383018
Bangaren kas ada kasa, Mame Biram Diou dan kwallon kafa a kungiyar Stock City a kasar England ya rasa mahaifiyarsa sakamakon abin da ya faru a lokacin aikin hajjin bana.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sports Mole cewa, Mame Biram Diou dan wasan kwallon kafa na kasar Senegal da buga wasa a kasar Birtanitya ya rasa mahaifiyarsa a cikin abin da ya faru.

Ginilan Diouf ta tafi aikin hajjin ne kamar sauran alahazai na kowace kasa da nufin safke farali, amma kuma sakamakon abin da aka aikata kan alhazan a Mina ta rasa ranta.

A kan hakan kungiyar kwallon kafa ta Stock City ta bayar da dama gad an wasanda ya tafi hutu, kuma ta sanar da sakon taziyya gare shi da danginsa baki daya kan wanann rashi da ya yi.

A cikin bayanin ya zo cewa, kungiyar kwallon kafa ta Stock City tana taya dan was anta alhinin rashin mahaifiyarsa, tare da bayyana bababn alhini da damuwa da abin da ya same shi tare da danginsa baki daya, kuma kungiyar tana yin fatan rahamar ubangiji ga mahaifiyarsa.

Mame Biram Diou musulmi ne dan kasar Senegal kuma fitaccen dan wasan kwallon kafa na duniya wanda ya buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United a lokutan baya.

3382814

Abubuwan Da Ya Shafa: birtaniya
captcha