IQNA

Babu Tattaunawa Da Amurka / Umarnin Kur’ani Na Tsorata Makiya Ya Tabbata A Kudancin Kasa

20:42 - October 07, 2015
Lambar Labari: 3383020
Bangare siyasa, Ayatollah Sayyid Ali Khameni a lokacin da yake ganawa da manyan kwamandojin rundunar kare juyin juya halin muslunci na ruwa da kuma ma’aikata a wannan bangare na kudancinkasar ya ce, umarnin kur’ani na saka tsoro a zukatan makiya ya tabbata a kudancin kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na ofishin jagora cewa, , a safiyar yau Laraba ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da kwamandoji da ma'aikatan sojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran da iyalansu bugu da kari kan iyalan shahidan sojojin ruwan, inda yayin da yake ishara da rawar da matasa ma'abota juyi na sojin ruwan dakarun kare juyin da kuma matasan kudancin kasar Iran wajen tabbatar da tsaron tekuna da kuma haifar da tsoro da fargaba cikin zukatan makiya ya bayyana cewar: Makiya dai suna kokari ne wajen sauya mahangar jami'an gwamnati da kuma tunanin mutane musamman matasan (kasar Iran). A saboda haka wajibi kowa da kowa yayi taka tsantsan.

A jawabin da ya gabatar a wajen wannan ganawar, Ayatullah Khamenei yayi ishara da muhimmancin da ke cikin batun tabbatar da tsaron teku, yana mai cewa: Wajibi ne a zama cikin shiri, kamar yadda Alkur'ani ya fadi, na haifar da tsoro da fargaba cikin zukatan makiya, ta yadda ba zai yi tunanin wuce gona da iri ba. Don kuwa matukar aka yi sako-sako, to kuwa makiyi zai kutso kai.

Jagoran ya ci gaba da cewa: A halin yanzu albarkacin kafa fage da sansanin juyin juya halin a kudancin kasar Iran da ya hada da sojin ruwa na dakarun kare juyi da kuma matasan kudancin kasa, lalle an tabbatar da wannan umurni na Alkur'ani na sanya fargaba da tsoro cikin zukatan makiya.

Jagoran juyin juya halin Musulunci kuma babban kwamandan dakarun kasar Iran ya jaddada cewar babu wani lokaci da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta taba zama mai tsokana da fara yaki. Jagoran ya ci gaba da cewa: To amma a koda yaushe dabi'ar makiya ta kasance dabi'a ce ta neman kutsowa da wuce gona da iri. A saboda haka wajibi ne a koda yaushe a dinga karawa da karfafa irin karfi na ilimi da kayan aiki da ake da shi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana kara irin karfin da sojin ruwa na dakarun kare juyi haka nan da dakarun ruwa na soji suke da shi a matsayin wani lamari da ya zama wajibi. Haka nan kuma yayin da yake jaddada wajibcin ci gaba da kiyaye ambaton matasa ma'abota imani da riko da tafarkin juyin juya hali irin su Shahid Nadir Mahdawi da abokansa wadanda cikin jaruntaka suka tsaya kyam a gaban jiragen ruwan yakin Amurka da dandana musu kuda, Jagoran ya ce: Sakamakon irin wannan jaruntaka da tsayin daka ne makiyan tsarin Musulunci suka fahimci cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran dai ba kanwar lasa ba ce da kowa zai iya yin abin da ya ga dama a kanta ba.

Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jinjinawa iyalai musamman matayen kwamandoji da ma'aikatan sojin ruwan saboda yadda suka kasance tare da mazajensu a wajajen aikin na su a kudancin kasar Iran.

A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi ishara da makirce-makircen da ma'abota girman kan duniya suke kullawa yankin nan inda ya bayyana cewar wadannan mutane ba sa jin kunyar amfani da duk wata hanya mai hatsarin gaske wacce ta saba wa dan'adamtaka wajen kashe mutanen da ba su ci ba su sha ba. Jagoran ya ci gaba da cewa: Ikirarin da suke yi na kare hakkokin bil'adama da hakkokin ‘yan kasa, karya ce kawai tsagoronta.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana harin da suka kai asibiti a kasar Afghanistan (cikin kwanakin nan) da zubar da jinin mutane a Siriya, Iraki, Yemen, Palastinu da Bahrain a matsayin wasu daga cikin misalan rashin imanin da tausayin ma'abota girman kan, daga nan sai ya ce: A yau mafi girman hatsarin da ke fuskantar duniya shi ne munafunki, riya da karyar masu ikirarin kare hakkokin bil'adama.

Ayatullah Khamenei yayi ishara da matsayi da rawar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take takawa a cikin irin yanayin da yankin nan yake ciki inda ya ce: A irin wannan yanayin, cikin taimakon Allah Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta samu nasarar hana tasirin makiya a cikin gida, haka nan kuma cikin wurare da dama ta hana makiyan cimma manufarsu a wannan yankin.

Haka nan kuma yayin da yake jaddada cewar irin rashin nasarar da makiya suke fuskanta a cikin Iran da sauran kasashen yankin nan ya samo asali ne sakamakon taka tsantsan, shirin ko ta kwana, azama matasa ma'abota juyin juya halin Musulunci da kuma tsayin daka da karfi Jamhuriyar Musulunci a yankin, Jagoran cewa yayi: A saboda haka ne mafi yawan kokari da tsare-tsaren ma'abota girman kai sun ginu ne wajen nuna kiyayya da gaba da tsarin Musulunci na Iran. A saboda haka ne ma ikirarin Amurka na son tattaunawa da Iran don neman samun kafar shiga da kutso kai ne.

Don haka ne yayin da yake sukar wasu masu karamin tunani na cikin gida da suka gagara fahimtar inda aka sa gaba, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce: A tattare da irin wadannan mutane masu karamar kwakwalwa akwai wasu mutanen kuma na daban wadanda maslaha ta kasar nan ba ta da wani muhimmanci a gare su.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da wasu maganganu da irin wadannan mutanen suke yi musamman dangane da batun tattaunawa da Amurka, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Wadannan mutanen suna fadin cewa yaya za a yi Imam Ali (a.s) da Imam Husaini (a.s) za su tattauna da makiyansu, to amma a halin yanzu a dinga adawa da tattaunawa da Amurka?

Yayin da yake ba da amsar wannan tambayar, Jagoran cewa yayi: Sharhi da kuma kwatanta irin abubuwan da suka faru cikin tarihin Musulunci da abubuwan da ke faruwa a halin yanzu a kasar nan, tsananin rashin hangen nesa ne. Don kuwa Imam Ali (a.s) da Zubair ko kuma Imam Husain (a.s) da Umar bn Sa'ad da irin wannan tattaunawa ta yau wato bani gishiri in ba ka manda suka yi ba. Face kowane guda daga cikin wadannan manyan bayin Allah ya sanya musu tsoro ne da kuma yi musu nasiha zuwa ga tsoron Allah.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Abin bakin cikin shi ne cewa wasu suna ta maganganu da rubutu cikin jaridu da bayyanar da wasu batutuwa dangane da tattaunawar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Babbar Shaidaniya (Amurka), wanda hakan babban kuskure ne.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar Iran ba ta adawa da asalin tattaunawa da kowace kasa, shin kasar Turai ce ko wacce ba ta Turai ba. Don haka sai ya ce: to amma dangane da Amurkan kan lalle lamarin ya bambanta. Don kuwa irin fassarar da suka ba wa tattaunawa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ma'anar hakan ita ce kutso kai da bude hanyar tilasta muradunta.

Haka nan yayin da yake ishara da aiki kafada da kafada tsakanin Amurka da sahyoniyawa wajen cutar da bil'adama, Jagoran cewa yayi: Tattaunawa da Amurka tana nufin bude hanyar kutsowarsu a fagen tattalin arziki, al'adu, siyasa da tsaron kasar nan.

Har ila yau yayin da yake ishara da tattaunawar nukiliya ta baya-bayan nan, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: A yayin wannan tattaunawar, bangaren da ake tattaunawar da shi yayi kokarin amfani da duk wata dama da ya samu wajen kutsowa da kuma yin wani abin da zai cutar da manufar kasar nan. Koda yake idanuwan jami'ai masu tattauna na Iran a bude suke. Amma duk da hakan Amurkawan sun samu wasu wajajen.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Tattaunawa da Amurka dai kan a'a. Don kuwa ba ma kawai tattaunawar ba ta da wani amfani ba ne, face dai tana da cutarwa mai yawan gaske.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Yanayin da ake ciki a halin yanzu, bisa la'akari da ayyuka da kokarin makiyan Jamhuriyar Musulunci ta Iran wanda muna da masaniya kan hakan, wani lokaci ne mai muhimmancin gaske. Don kuwa abin da suke so shi ne sauya lissafin jami'an gwamnati da sauya tunanin mutane musamman kan lamurran da suka shafi juyin juya hali, addini da maslaha ta kasa.

Dangane da batun sauya tunanin mutane, Jagoran ya bayyana cewar babban wadanda suke hari su ne matasa don haka sai ya kirayi matasan da su yi taka tsantsan yana mai cewa: Koda yake cikin yardar Allah, matasanmu a jami'oi ne ko kuma wadanda suke cikin soji a farke suke suna ci gaba da ayyukansu. Don haka a wannan bangaren kan ba ni da wata damuwa.

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da zagayowar shekarar Mubahala da tsayin dakan da Manzon Allah (s.a.w.a) da Iyalan gidansa suka yi wajen tinkarar ma'abota kafirci. Don haka sai ya kirayi matasa ma'abota riko da juyi da cewa: Kamar yadda ya faru a lokacin Mubahala a farko-farkon Musulunci inda dukkanin imani ya fito wajen tinkarar kafirci dukkaninsa, haka nan kamar yadda a wancan lokacin haifa da hasken Ma'aikin Allah (s.a.w.a) tare da Iyalansa suka yi nasara a kan makiya, a yau ma al'ummar Iran albarkacin imani da riko da koyarwar Ubangiji, za su fatattaki makiya daga fage.

A karshen jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Matukar muka tsaya kyam wajen taimakon addinin Allah, ko shakka babu Allah zai cika alkawarinsa na taimakon wanda ya taimaki addinin Allah. Makiyan tsarin Musulunci kuwa za su sha kashi cikin makirce-makircensu na soji, tattalin arziki, liken asiri da al'adu.

Kafin jawabin jagoran, sai da babban kwamandan sojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musuluncin na Iran Admiral Fadawi ya gabatar da jawabinsa inda yayin da yake ishara da irin nasarorin da dakarun kare juyin juya halin Musuluncin suka samu a lokacin kallafaffen yaki ya bayyana cewar: Sojojinka suna jiran umurninka ne don su koya wa Babbar Shaidaniya darasi da dandana musu kuda.

Admiral Fadawi ya kara da cewa dakarun nasa suna cikin shirin da ya kamata, don haka sai ya ce: Gwada wani bangare na irin karfi da shirin da sojin ruwa na dakarun kare juyin suke da shi, lamari ne da ya sanya makiya fara maganar sauya irin tsarin da suke da shi. Alhali kuwa abin da suka gani daga gare mu, ba za a taba kwatanta shi da abin da ba su sani ba na abin da muke da shi.

3382718

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha