IQNA

Cibiyar Kula Da Wurare Masu Tsarki A Iraki Ta Fara Shirin Kula Da Masu Ziyarar Arbain

16:53 - October 08, 2015
Lambar Labari: 3383155
Bangaren kasa da kasa, cibiyar da ke kula da wurare masu tsarki a kasar Iraki ta fara shirin samar da wurare 30 na koyar da karatun kur’ani mai tsarki ga masu ziyarar arbain.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar hubbaren Alawi cewa, a cikin wani bayani da ta fitar jiya cibiyar da ke kula da wurare masu tsarki a kasar Iraki ta fara shirin samar da wurare 30 na koyar da karatun kur’ani mai tsarki ga masu ziyarar arbain mai lakabin Fatiha a wannan shekara.

Amir Ka’abi shi ne shugaban wannan shiri, ya bayyana cewa sun dauki wannan mataki ne domin kara inganta lamurra da suka shafi karatun kur’ani mai tsarki d akuma kyautata shi a tsakanin masi gudanar da aikin ibada na ziyara.

Ya ci gaba da cewa bisa la’akari da cewa lokacin gudanar da ziyarar takaitacce ne, amma za a iya yin amfani da dama domin amfana da lokacin wajen raya lamarin kur’ani mai tsarki domin samu ladar.

A kowace shekara dai miliyoyin mutane ne suke ziyartar tarukan arbain na shhahadar Imam Hussain a hubbarensa mai tsarki, domin gudanar da taruka na ziyara a wannan rana, wamnda hakan kan zo bayan kwanaki arbain na shahadarsa.

Da dama daga cikin jami’a maus kula ayyukan sun nuna gamsuwarsu kan wannan shiri, wanda zai kunshi wrare 30 da aza  kebe domin gudanar da shirin na kur’ani mai tsarki da kuma koyar da sahihin karatu na taikaccen lokaci.

3382776

Abubuwan Da Ya Shafa: iraki
captcha