Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na OnIslam cewa, Jafar Seganda shugaban cibiyar lauyoyi masu kare hakkokin musulmi a kasar Uganda ya bayyana cewa suna kokarin ganin sun fahimtar da wasu mummaunar fahimta dangane da abin da ake yada musu kan addinin muslunci a aksar.
Ya ci gaba da cewa cibiyarsa tana da shirye-shirye da dama kan hakan, kuma tuni ta fara aiwatar da wasu daga cikinsu da nufin cimma wannan burin a fahimtar da mutane hakinanin addinin muslunci, ba a bin da suka saba ana gaya musu dangane da shi daga wasu wadanda ba musulmi ba.
Kasar Uganda dai na daga cikin kasashen gabacin nahiyar Afirka da suke da yawan musulmi da suke bin koyarwar addaini, duk kywa da cewa dai mafi yawan mutanen kasar mabiya addinin kirista ne, amma musulmi su ne na biyua kasar.
Tun bayan abubuwan da suka faru da ake kokarin danganta su da addinin muslnci da suke da alaka da ayyukan ta’addanci, wasu daga cikin mabiya addinin kirista a kasar sun samu mummunar fahimta kan muslunci.
Ya kara da cewa babbar manufar shirin cibiyar tasa shi ne kokarin bayyana hakikanin koyarwar muslunci ta haklika, wadda ta ginu kan zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin muslunci da sauran addini da kuma girrmama dan adam.
Daga cikin abubuwan da ake yi kuwa har da daukar nauyin masu wa’azi a masallatai, da kuma samar da wasu shirye-shirye na tashoshin talabijin da kafafen yada labarai na sadarwar yajnar gizo da sauransu.
3383669