IQNA

ISESCO Ta Yi Allawadai Da Hare-Haren Ta’addanci Na Birnin Ankara

23:47 - October 12, 2015
Lambar Labari: 3384726
Bangaren kasa da kasa, kngiyar raya harkokin ilimi da al’and muslunci ta ISESCO ta yi Allawadai da kakkausar murya kan harin birnin Ankara na kasar Turkiya.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya naakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na isesco.org.ma cewa, kungiyar ta ISESCO ta yi kakkausar kan wannan hari na birnin Ankara, tare da bayyana shi a matsayin wani ynkuri na haifar da fitina a kasar.

Dubban mutane sun yi taro a birnin Ankara na kasar Turniya domin  karram wanda harin ta’addanci ya kashe a jiya asabar. Mutanen sun taru ne a dandalin Saihiyya da ke kusa da tashar jirgin kasar da aka kai harin jiya wanda ya ci rayukan mutane.

A jiya asabar ne dai wasu ‘yan kunar bakin wake biyu su ka kai hari akan taron zaman lafiya da masu ra’ayin sauyi da rajin kare hakkin bil’adama su ka shirya a birnin Ankara.

Kawo ya zuwa yanzu babu wata kungiya wacce ta dauki alhakin kai harin na jiya, sai dai mahukuntan kasar suna zargin ‘yan ta’adda. Mutane 95 ne su ka rasa rayukansu yayin da wasu daruruwan kuma su ka jikkata.  

Adadin Mutanan da suka rasu sanadiyar harin ta’addancin da aka kai birnin Ankara na kasar Turkiya a jiya Assabar ya haura zuwa 97.

Ma’aikatar Piraministan kasar ta sanar da cewa Mutanen da su ka rasu a sanadin harin ta’addancin ya haura zuwa casein da biyar.

An kai harin ne adaidai lokacin da ‘yan hamayyar siyasa su ke taruwa a bakin wata tashar jirgin kasa domin gudanar da Zanga-zanga.

Piraministan kasar  ya bayyana cewa a yayin harin a kwai mutane fiye da dubu sha hudu a gurin.

Shidau wannan hari an kai shi ne a daidai lokacin da kasar ke shirye-shiryen gudanar da zabe a ranar daya ga watan Nuwanba mai kamawa.

Gwamnatin kasar ta ware kwanaki uku na zaman makoki domin girmama wadanda suka rasun.

Ya zuwa yanzu babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, da kuma wasu kasashen duniya ciki kuwa har da Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun yi alawadai da wannan ta’addanci.

3383919

Abubuwan Da Ya Shafa: isesco
captcha