IQNA

Za A Gudanar Da Taron Tadabbur Kan Kur’ani Mai Tsarki A Kasar Morocco

21:18 - October 13, 2015
Lambar Labari: 3385196
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani taro mai taken yin tunani kan ayoyin kur’ani mai tsarki a cikin wannan wata a birnin Kazablanka na kasar Morocco.


Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na ynar gizo na Sabaq cewa, wannan taro zai gudana ne a jami’ar Hassan Sani da ke kasar a bangaren ilimin adabi.

Kimanin masana 400 daga sassa na kasar da kuma kasashen ketare za su samu halartar wanann zaman taro wanda zai yi dubi kan lamurra da dama da suka shafi kur’ani mai tsarki da kuma muhimman darussan da yake koyar da dan adam.

Umar Bin Abdullah Al-muqbil shugaban cibiyar raya zurfafa tunani kan koyarwar ayoyin kur’ani mai tsarki ya bayyana cewa, wannan taron yana daya daga cikin irinsa masu matukar muhimmanci da aka taba gudanarwa, tare da halartar fitattun mutane na kasashen duniya kan lamurran kur’ani.

Ya ci gaba da cewa hakika kur’ani mai tsarki yana dauke da muhimman darussa da yake koyar da dan adam a cikin dukkanin lamiurra da suka shafi rayuwarsa, wanda kuma mutum ba zai iya kaiwa ga irin wadanna ilmomi na kur’ani ba sai da tunani abin da ake kira tadabbur a cikin ayoyinsa.

Dangane da yadda hakan ke yin tasiri kuwa yana da alaka ne da mutum shi a kan kansa a matakin farko, kafin daga bisa lamarin da ya danfaru da bangaren yanayin zamantakewarsa, wato wuri da kuma al’umma da yak erayuwa a cikinsu.

Mutum zai iya tasirantuwa da koyarwar kur’ani amma yanayin da yak erayuwa a cikinsa ya zama yana da banbanci da abin da ya ilmantu da shi, hakan yakan kawo mutum nakasu a wasu bangarorin, amma idan ya samu kansa a cikin al’umma mai bin koyarwar kur’ani, to zai aiwatar da abin da ya koya.

Wanann cibiya dai ta dauki tsawon shekaru kimanin hudu tana gudanar da ayyukanta tun bayan kafa a cikin shekara ta 1433, kuma tana tafiyar da ayyukanta ne tare da hadin gwiwa da sauran mambobinta na kasashen musulmi.

3384205

Abubuwan Da Ya Shafa: Moroco
captcha