IQNA

Wasu Jami’an UN Sun Yi Allawadai Da Halasta Jinin Yan Shia’a Da Wasu Wahabiya Suka Yi

22:38 - October 14, 2015
Lambar Labari: 3385724
Bangaren kasa da kasa, wasu manyan jami’an mjaliasar dinkin duniya sun yi Allawadai da kakkausar murya dangane da wasu fatawoyi na kafirta mabiya mazhabar shia da kuma kiristoci da wasu wahabiyawan Saudi suka yi.

Kamfanin dillancin labaran Iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na PressTV cewa, Babbar mai baiwa majalisar dinkin duniya shawara kan lamarin kisan kiya Adama Ling, da kuma Jenifer Walch sun bayyana takaicinsu matukan wasu fatawoyi da wasu masu kafirta musulmi suka bayar da ke halasta jinin shia da kiristoci a Syria.

 

Manayna jami’an biyu suka ci gaba da cewa idan har za a samu wasu mutane su fito karar suna yin irin wadannan magnganu na ta’addanci da kuma yin kira karara da sunan wani addini da a zubar da jinin wasu, to hakan ya nuna akwai babbar matsala.

Suk ace ya zama wajibi a kan gwamnatocin irin kasashe da su dauki mataki a aikace wajen shiga kafar wando daya da irin wadannan mutane da abin da suke aikatawa, tare da taka musu birki da ma hukunta su, domin hakan shi ne babban abin da ya haifar da ta’addancin da ya addabi dubiya a halin yanzu.

 

Gwamnatin Saudiyya dai ba ta ce uffan kana bin da wasu malaman wahabiya na kasar suka ce ban a halasta jinin musulmi shia da kuma kiristocia  kasar Syria, tare da bayyana kisan wadannan matsayin wani abu mai tsarki a mahangar akidarsu.

Tun kafin wannan lokacin dai dama gwamnatin ta SDaudiyya ba ta boye cewa it ace ke taimaka ma ‘yan ta’adda a cikin kasar Syria ba, kuma hakan yana da alaka ne da akidar da gwamnatin kasar ta ginu a kanta ta yin biyayya ga manufofin turawa tare da sabawa duk wanda ya saba musu, a lokaci guda kuma suna raya muslunci har ma da kafirta wasu.

 

Yakin Syria dai an fara shi ne tn cikin watan Maris 2011, ya zwa yanzu kimaini mutane dubu 250 ne suka rasu, wasu miliyoyi kuma sun zama yan gudun hijira.

3385531

Abubuwan Da Ya Shafa: UN
captcha