Kamfanin dillancin labaran Iqna ya harbata cewa, tashar talabijin ta LAMPE FALL a kasar Senegal da ke da alaka da masu bin tafarkin dariku a kasar, ta yi Allawadai da abin da ya faru a Hajji 2015 ta hanyar watsa wani shiri kan hakan.
An watsa wannan shiri ne kai tsaye daga karfe 16 zuwa 17 na yamma, tare da halartar Sharif Mbalo, shugaban cibiyar Al-yasin ta kasar Senegal, Muhammad Baru wani dan jarida, Sheikh Huna Fay daya dag acikin daraktocin hukumar alhazai ta kasar Senegal, Abdullah Babading daya daga cikin fitattun marubuta na kasar.
Wadanda suka halarci wannan shiri musamman Sharif Mbalo wanda daya ne daga cikin mabiya tafarkin Ahlul bait (AS) a kasar, sun nuna takaici matuka dangane da abin da ya faru da mahajjata awannan shekara ta hanyar yin aikin da ya zubar da mutuncin masu daukar bakuncin wannan ibada mai girma.
3390504