IQNA

Gwamnatin Masar ta Dauki Tsararan matakai Na Takura Ma 'yan shi'ar A Ranar Ashura

23:00 - October 21, 2015
Lambar Labari: 3391458
Bangaren kasa da kasa, Ma'aikatar da ke kula da harkokin addini a kasar Masar ta sanar da cewa ta dauki tsauraran matakai domin ganin hana yan shi'a yina bin da ya saba addini a masallacin R'asul Hussain (AS) da ke Alkahira.


Kaafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Yaum Sabi cewa, Sheikh Muhammad Abdulrazak mataimaimakin ministan ma'akatar kula da harkokin addini a kasar Masar ya bayyana cewa, sun bayar da umarni ga masu kula da masallacin R'asul Hussain (AS) da ke kasar a ranakun Tasu'a da Ashura, inda ya ce suna yin abubuwan da suka saba wa koyarwar addini.

Ya ci gaba da cewa wanan yana da cikina ikinsu daukar matakai da suka dace domin shawo kan 'yan shi'ar wajen ganin ba su ci gaba da yin abin da ya sabawa addini a wannan masallaci na Ra'asul Hussain (AS).

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun irin wadannan matakai da ake dauka kan mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah ba a kasar ta Masar, domin kuwa da dama daga cikin gwamnatocin da akyi a baya-bayan nan musamamn sun dauki irin wanann mataki.

Masallacin Ra'asul Hussain (AS) dai yana daga cikin wurare da mabiya tafarin shi'a suke ziyarta a ranakun tunawa da shahadar Imam Hussain (AS) a cikin kwanaki muharram da ake raya su domin tunawa da shahadarsa da kuma sadaukrwarsa.

Yanzu haka haka mabiya tafarkin iyalan gidan manzoa  koina suna raya wadannan ranaku nab akin ciki da tunawa da musibar da ta samu iyalna gidan amnzo a lokacin da suke ta tare da Imam Hussain (AS) a cikin wadannan ranaku na wanann wata.

3391161

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha