Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «almasalla.trave» cewa, a jiya ne fara gudanar da wani zaman taro wanda yake da taken Haliful Kur’an wato mabocin kur’ani mai tsarki tare da hadin gwiwa da cibiyar kula da hubbarorin Imam Hussain da Hadrat Abbas (AS) a kasar Iraki.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro yana mayar da hankali ne kan muhimamn lamurra da suka shafi koyarwar kur’ani mai tsarki da kuma yadda hakan zai zama a bin koyi ga musulmi, ta yadda zai yi tasiri wajen mayar da wannan al’umma ta zama tana tafiya kan sahihin tafarki.
Sheikh Qase Alhasnawi shugaban cibiyar Hubaren Zaid Shahid (AS) ya bayyana cewa, akwai alaka mai karfi tsakanin yunkurin Imam Hussain (AS) da kuma yunkurin Zaid Shahid (AS) wanda hakan ya zama wata bababr fitila mai haskaka azzalumai kowa ya gane su.
Shi ma a nasa bangaren sheikh Karrar Alkasimi ya bayyana cewa, abin da Zaid Shahid (AS) ya yi yunkuri ne na yin umarni da kyakkyawa da kuma hani daga mummuna, kaar yadda Imam Hussain (AS) da sauran iyalan gidan amnzo da sahabbansu suka yi a Karbala.
Zaid Bin Ali Bin Hussain (AS) da Imam Sajjad (AS) ne, kuma ya kasance daya daga cikin mabiya tafarkin limaman gidan amnzon Allah nag aba-gaba, wanda ya sadaukantar da rayuwarsa domin yaki da azzalumai da suke cutar da iyalan gidan manzon Allah da sauran bayin Allah a zamaninsa.
3421602