IQNA

Tattanawa Da Amurka Kan Yankin Ba Shi Da Ma’ana / Tawagar Masu Tattaunawa Na Kare Manufofin Kasa

19:00 - November 03, 2015
Lambar Labari: 3443167
Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya hali ya bayyana cewa; Amurka tana son ta yi amfani da batun tattanawa kan lamurran yanking abas ta tsakiya ne domin ta samu damar aiwatar da manufofinta, inda kasha 60 zuwa 70 manufofinta ne kawai, sauran kuma za ta aiwatar da su hanyar da ta sabawa doka, Kenan tattaunawa wace ma’ana keg are ta?


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jagora na yanar gizo cewa, a safiyar Lahadi ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da ministan harkokin waje, jakadun (Iran a kasashen waje) da manyan jami'an ma'aikatar harkokin waje na Jamhuriyar Musulunci ta Iran inda ya bayyana ci gaba da riko da tushe da tubalin siyasar waje na Iran kamar yadda ya zo cikin kundin tsarin mulki a matsayin ingantacciyar hanya wacce kuma ta yi daidai da hankali da Iran ta rika wajen magance batutuwa masu muhimmanci da suka shafi wannan yanki irin su abin da ke faruwa a kasashen Siriya, Yemen da Bahrain. Daga nan sai ya ce: Manufar Amurka a yankin nan, ta yi hannun riga da manufar Iran.

Ayatullah Khamenei ya bayyana siyasar harkokin waje na Iran da cewa ita ce dai wannan siyasa ta waje da ta zo cikin kundin tsarin mulki na kasar. Daga nan sai ya ce: Wannan siyasar ta waje dai ta samo asali ne daga koyarwar Musulunci da kuma manufa da koyarwar juyin juya halin Musulunci. A saboda haka jami'an ma'aikatar harkokin waje da jakadu da ma'aikatan diplomasiyyar (Iran a waje), a hakikanin gaskiya wakilai, sojoji kana kuma masu hidima ne ga wadannan koyarwar.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Siyasar harkokin wajen (Iran), tamkar sauran dukkanin kasashen duniya, ta ginu ne bisa kiyaye manyan manufofin da aka ginu a kai. Don haka zuwa da tafiyar gwamnatoci ko kuma zauki na siyasa ba zai sauya komai ba. Don kuwa gwamnatoci cikin gudanarwa da tsare tsare ne suke da tasiri da kuma bakin magana.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Wajibi ne dukkanin tsare-tsaren gudanarwar da diplomasiyyar gwamnatoci daban-daban su zamanto wajen ciyar da tushen siyasar waje da ya zo cikin kundin tsarin mulki gaba. A saboda haka wajibi ne wakilan siyasar wajen Iran a kasashen waje, su dauki kansu a matsayin wakilai kana kuma masu ba da kariya da dukkanin karfinsu ga siyasar wannan tsarin.

Har ila yau yayin da yake ishara ga irin bakar farfagangar da makiya suke yadawa kan abin da suke kira tilasta wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran sauya siyasar wajenta, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Wadannan maganganu da Turawan yammacin suke fadi, a hakikanin gaskiya sun samo asali ne sakamakon irin damuwar da suke ciki dangane da irin yadda Jamhuriyar Musulunci ta Iran, alal akalla a yanayi na yankin nan, ta hana manyan kasashe ‘yan mulkin mallaka musamman Amurka cimma manufofinsu. A saboda haka ne a koda yaushe suna fatan ganin an sauya wannan siyasar.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana siyasar Amurka a wannan yankin mai matukar muhimmancin gaske na yammacin Asiya a matsayin ummul aba'isin irin matsalolin da suka kunno kai a yankin, don haka sai ya ce: Sabanin mahangar wasu mutane, Amurka ita ce tushen mafi yawa daga cikin matsalolin yankin nan, ba wai wani bangare na maganin wadannan matsalolin ba.

Haka nan yayin da yake sake jaddada cewa sisayar wajen Jamhuriyar Musulunci ba tsari da gini na wane da wane ba ne, face dai ya samo asali ne daga kundin tsarin mulki na kasar, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Cikin kundin tsarin, an bayyana addinin Musulunci a matsayin ma'aunin siyasar harkokin waje. A saboda haka wajibi ne mahanga da matsayar da za a dauka dangane da kasashe da kuma batutuwa daban-daban, wajibi ne su zamanto sun samo asali ne daga addini.

Har ila yau yayin da yake ishara da wani tushe na siyasar harkokin wajen na Iran da ya zo cikin kundin tsarin mulkin ciki kuwa da suka hada da goyon bayan da nuna ‘yan'uwantaka ga dukkanin musulmin duniya, taimako da goyon bayan raunanan duniya, yin watsi da mulkin mallaka da kuma hana tasirin ‘yan kasashen waje a dukkan fagage, kiyayen ‘yancin kai na kasa, kare hakkokin dukkanin musulmi, rashin mika kai ga ‘yan mulkin mallaka, alaka mai kyau da gwamnatocin da ba a rikici da su, nesantar kowane irin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan al'ummomi da kuma goyon bayan gwagwarmayar neman hakki da raunana suke yi wajen tinkarar ma'abota girman kai a duk inda suke a duniya, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Wadannan koyarwa masu kyau, wani lamari ne da ya ke janyo hankulan al'ummomi musamman masanan cikinsu.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Siyasar waje ta Jamhuriyar Musulunci da irin wadannan siffofi, wata siyasa ce ta juyin juya hali. Idan har aka sanya basira cikin gudanar da wadannan siyasar, to kuwa za a ga gagarumin tasirinta, sannan kuma za ta zamanto tana da karfin magance manyan matsaloli kuma masu muhimmanci na duniyar musulmi.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da wasu tasirin wadannan siyasar da aka gani, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa yayi: Aiwatar da siyasar juyin juya hali a dukkanin fagage ciki kuwa har da fagen diplomasiyya wani lamari ne da zai kara irin karfi da tasirin da ake da shi, bugu da kari kan daga matsayin kasar da kuma al'ummar Iran a tsakanin al'ummomi.

Har ila yau yayin da yake jaddada wajibcin ci gaba da riko da wadannan siyasa ba tare da tsayawa ba, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Ba ma ikirarin mun cimma dukkanin manufofin da muke son cimmawa, kai hatta kusatar haka ma ba ma yi, don kuwa siyasar wajen a fagen aiki ta fuskanci wasu matsaloli da suka hada da gafala, rashin aiki tukuru, nuna karancin basira da kuma wasu kafar ungulu na wasu kasashen waje. To amma irin daukakar da kasar nan take da ita a halin yanzu, ta samo asali ne albarkacin wannan siyasa da ke cike da hikima. Idan kuwa da a ce ba mu yi aiki da wannan koyarwar ba, Allah kawai ya san irin matsaloli da wahalhali masu ban mamaki da za mu fuskanta.

Yayin da yake magana ta gaba daya dangane da wannan bangare na jawabin nasa, Ayatullah Khamenei ya kirayi jami'an ma'aikatar harkokin wajen da jakadun Iran a kasashen waje da cewa: Ku ci gaba da riko da kuma aiwatar da koyarwar wannan juyi da kuma tabbatacciyar siyasar waje na Iran da dukkan karfinku, don makiya ‘yan kasashen waje da ‘yan amshin shatansu na cikin gida su yanke kaunar samun wani sauyi cikin siyasar wajen Jamhuriyar Musulunci.

A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi karin haske kan irin abubuwan da za a iya fuskanta da kuma abubuwan da ya wajaba a yi sakamakon riko da wadannan koyarwar.

Jagoran ya bayyana cewar: Ku kula da cewa wajibi ne tsarin gudanarwar siyasar harkoki ta zamanto karkashin tushen wadannan koyarwar, ba wai ku yi abubuwan da suke kishiyartar wadannan koyarwar da sunan tsari da dabatar aiwatar da wadannan koyarwar ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana "dogaro da kai da kuma fitowa fili da tsayin daka wajen tinkarar dukkanin abubuwan da suke kawo cikas" a matsayin wasu daga cikin wajiban siyasar harkokin waje. Daga nan sai ya ce: Dabatar siyasar waje ita ce ku yi dukkanin abin da za ku iya bayanin wadannan siyasa da kuma abubuwan da suke kawo musu cikas.

Jagoran ya bayyana mahangar Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da batutuwan da suka shafi yankin nan da cewa wata mahanga ce mai karfin gaske, sannan kuma yayin da yake bayanin cewa mahangar Iran ita ce hanyar magance matsalolin da yankin nan yake fuskanta, Jagora cewa yayi: Dangane da batun Palastinu, a yayin da muke kore samun haramtacciyar gwamnatin Sahyoniyawa da kuma yin Allah wadai da irin danyen aikin da take aikatawa a kowace rana, mun ba da shawarar a gudanar da zaben da dukkanin al'ummar Palastinu za su shigo ciki, wanda hakan yayi daidai da irin ma'auni na duniya.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Duk wata gwamnatin da al'ummar Palastinu suka zaba, ita ce za ta ayyana makomar sahyoniyawa da mazauna yankunan Palastinu da aka mamaye. Koda yake don nuna adawarsu da wannan shawara da muka bayar sun bayyana cewar hakan ai yana nufin rushewar wannan haramtacciyar gwamnati; wanda ai wajibi ne wadannan haramtacciyar gwamnati ta ruguje.

Dangane da kasar Siriya kuwa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Mahangarmu ita ce mahanga mafi dacewa da hankali. Mu dai mun yi amanna da cewa babu wata ma'ana cikin wasu kasashe su zauna a tsakaninsu su zaba wa wani tsari na shugabanci irin yadda za a gudanar da shi da kuma matsayin shugaban wannan gwamnatin. Wannan wata bidi'a ce mai hatsarin gaske, da babu wata gwamnati a duniyan nan da za ta amince da hakan.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Hanyar magance rikicin kasar Siriya ita ce hanyar zabe. Don aiwatar da hakan kuwa, wajibi ne a kawo karshen irin taimako na kudi da makamai da ake ba wa ‘yan adawa. Da farko su amince da zaman lafiya da kawo karshen yaki, don mutanen Siriya su sami damar gudanar da zaben cikin yanayi na aminci da tsaro. Su zabi duk wanda suke so.

Har ila yau yayin da yake yin watsi da siyasar rarraba kasashe da mai she su ‘yan wasu kananan yankuna na kabilu, Jagoran cewa yayi: Batun ba wa wata kungiyar masu dauke da makami ikon fadi a ji da kuma kafa gwamnati, wannan ba abin amincewa ba ne. Aiwatar da wannan aikin, ba abin da zai haifar in ban da ci gaba da yakin.

Dangane da kasar Iraki kuwa, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Rarraba wannan kasar zuwa ga yankunan larabawa ‘yan Shi'a, larabawa ‘yan Sunna da Kurdawa, hakan wani lamari ne da yayi hannun riga da amfani da manufofin al'ummar kasar. Wani lamari ne maras ma'ana wanda kuma ba za a taba amincewa da shi ba.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Hadin kan dukkanin kasar Iraki da kuma dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali, ita ce hanyar magance matsalar kasar Iraki a mahangar Iran.

Dangane da kasar Yemen kuma, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewar: Kawo karshen wuce gona da irin Saudiyya a kasar, da kuma fara tattaunawa tsakanin al'ummar Yemen, lamari ne da zai iya kawo karshen rikicin da ke faruwa a kasar.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Abin da Saudiyya take yi a Yemen da Siriya, wata yaudara ce kawai. Dangane da kasar Yemen suna cewa suna kai hari kasar Yemen ne bisa bukatar shugaban kasar Yemen da yayi murabus wanda kuma ya gudu. To amma dangane da kasar Siriya kuwa ba a shirye suke su amince da bukatar halaltaccen shugaban kasar na su daina goyon bayan ‘yan adawa masu dauke da makami ba.

Dangane da kasar Bahrain kuwa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Mutanen kasar Bahrain babu wani abin da suke bukata dama da hakkinsu na zaben abin da ya dace da su. Mu kuwa muna ganin wannan bukata tasu wata bukata ce da ta yi daidai da hankali.

Bayan da yayi bayanin mahangar Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da hanyoyin da za a iya magance matsalolin wannan yankin, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Ummul aba'isin din dukkanin wadannan tashin hankali da rashin zaman lafiya shi ne goyon bayan da Amurka take ba wa haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma kungiyoyin ‘yan ta'adda. Wannan siyasar kuwa ta yi hannun riga sama da kasa da siyasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Haka nan kuma yayin da yake watsi da batun tattaunawa da Amurka kan matsalolin da suka shafi yankin nan, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Amurkawa dai suna son tilasta manufofinsu ne, ba wai magance matsalolin da ake fuskanta ba. Suna so ne su tilasta kashi 60 zuwa 70 na bukatunsu a yayin tattaunawar, sannan sauran manufofin na su kuma su tabbatar da su ta sauran haramtattun hanyoyi. Don haka wata ma'ana tattaunawar take da ita?

A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran ya sake jaddada maganar da ya sha yi dangane da kyautata alaka da kasashen makwabta, kasashen musulmi da kasashen Afirka a matsayin daya daga cikin siyasar wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jinjinawa tawagar Iran wajen tattaunawar nukiliya da manyan kasashen duniya yana mai cewa: Jin karfi da kuma zama teburi guda da manyan kasashen duniya da nufin kare manufofin Iran, wani bangare ne na irin karfi kana kuma abin yabawa na jami'an Iran a wajen tattaunawar ta nukiliya.

Har ila yau Jagoran ya sake jaddada wajibcin kiyaye manufofi na kasa yayin aiwatar da yarjejeniyar nukiliya da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, kamar yadda kuma ya gabatar da wasu nasihohi da kiraye-kiraye ga jakadun kasar Iran a sauran kasashen duniya wajen kula da kuma kiyaye manufofi da kuma daukaka ta kasar Iran.

Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci sai da ministan harkokin wajen Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya gabatar da jawabinsa inda yayi ishara da ayyukan da ma'aikatar tasa ta aikata da kuma shirin da take da shi wajen aiwatar da umurnin Jagoran juyin juya halin Musulunci dangane da yarjejeniyar nukiliya kamar yadda ya zo cikin wasikar da ya aike wa shugaban kasar ta Iran.

3428231

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha