Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ala-alam cewa, an kame mutane 45 masu neman sauyi a yankunan kasar.
Masarautar kasar Bahrain ta kame mune a yankuna 22 na kasar, kamar yadda kuma suka sake kame shugaban babbar cibiyar kare hakkin bil adama mai zaman kanta a kasar, bayan da ya soki mahukuntan kasar dangane da yadda suke cin zarafin 'yan adam a gidajen kaso.
rahotanni sun tabbatar da cewa da yammacin ya Alhamis ne jami'an tsaron masarautar ta Bahrain suka kai samame a gidan inda suk yi awon gaba da shi a cikin iyalansa, kuma babu bayani dangane da inda suka nufa da shi.
aya ne daga cikin fitattun larabawa masu fafutuka wajen kare hakkokin jama'a da ake zalunta a cikin kasashen larabawa, ya kuma shiga gidan kaso a lokuta daban-daban, sakamakon sukar lamirin masarautar Bahrain, kan cin zarafin dan adam da take yi, musamamn ma fursunonin siyasa da take tsare da su.
Kasar Bahrain na daga cikin kasashen larabawa da ke bin salon mulkin mulukiyya, ta yadda al'ummar kasa ba su da ta cewa a sha'anin mulkin kasa da siyasarta da kuma yadda za a tafiyar da ita, kamar yadda sarki da iyalansa da danginsa ne kawai ke da hakkin yin sarrafa arzikin kasa yadda suke so, kamar dai yadda lamarin yake auran kasashen larabawan yankin tekun fasha.