IQNA

Mai Bayar Da Fatawa A Quds Ya Yi Gargadi Dangane Yada Kur’ani Mai Kure

20:20 - November 05, 2015
Lambar Labari: 3443853
Bangaren kasa da kasa, babban mai bayar da fatawa a birnin Quds ya yi gargadi dangane da yada wani kr’ani da aka buga da kura kurai a cikinsa.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Ma’a cewa, Sheikh Muhammad Hssain babban mai bayar da fatawa a birnin Quds, kuma shugaban majalisar malaman Palastine ya yi gargadi dangane da yada wani kr’ani da aka buga da kura-kurai a cikin bugunsa ta hanyar share wasu ayoyi ko kuma maimaita wasu.

Ya ce an buda wadannan kwafi-kwafi na kur’ani mai tsarki ne a madaba’antar darul bayan da suke dauke da kure.

Shugaban majalisar malaman Palastine y ace akwai wadannan kura kurai ne a cikin shafi na 322, inda aka maimaita su, sai kuma acikin surat Ra’ad inda a nan ma an yi wasu kura-kuran da ya kamata a ce an yi la’akari da su.

Sheikh Muhammad Hussain ya yi kira ga dukaknin mutanen da suka samu wadannan kur’anai, da kuma cibiyoyi na addini da aka raba musu da su tattara su a kawo su cibiyar da ke kula da bayar da fatawa, domin kada a yi amfani da su  a cikin kure.

Daga karshe ya ce ya zama wajibi ga cibiyoyi da kuma madaba’antu da suke buga kur’ani mai tsarki da su rika sa lura yadda ya kamata.

3443766

Abubuwan Da Ya Shafa: quds
captcha