Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jagora cewa, a safiyar Talata ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Ozma Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubban daliban makarantu da na jami'oi na Iran inda ya bayyana gwagwarmayar al'ummar Iran da girman kan duniya a matsayin wata gwagwamaya "wacce ta dace da hankali wacce kuma ta ginu bisa kwarewa ta tarihi. Haka nan kuma yayin da yake ishara da matsalolii da cutarwar da Iran ta fuskanta sakamakon dogaro da Amurka da nuna rashin ya kamatan wasu ‘yan siyasar kasar a baya, Jagoran ya bayyana cewar: Amurkan (yau), ita ce dai Amurkan shekarun baya. To amma wasu mutane saboda wata manufa ko kuma saboda karamin tunani suna kokari sanya mutane su manta ko kuma gafala da wannan babbar abokiyar gaba kuma Makira. Ta yadda Amurkan za ta sace cutar da mu a duk lokacin da dama ta samu.
A yayin wannan ganawar wanda aka yi ta don tunawa da ranar 13 ga watan Aban, wato ranar kasa ta fada da ma'abota girman kan duniya, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana wannan zamani da ake ciki a matsayin zamanin tabbatar da daukaka ta kasa da shata taswirar ci gaban al'ummar Iran. Don haka sai ya bukaci al'umma musamman matasa da su fadaka da kuma amfani da basirarsu wanda hakan lamari ne mai muhimmancin gaske.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Abin da ke da muhimmanci cikin fahimta da yin sharhi kan yanayin da kasar nan take ciki da kuma tsara makomarta shi ne fahimtar cewa fadar da Jamhuriyar Musulunci da kuma al'ummar Iran suke yi da girman kan duniya, sabanin maganganun da wasu suke yi, ba wani yunkuri na rashin hankali ba ne, face yunkuri ne da ya ginu bisa tushe na hankali da kwarewa da kuma ilimi.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da cewa lura da irin kwarewar da ake da ita tana hana fadawa tarkon kura-kurai da yin ayyuka ba tare da lissafi ba, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Idan ma har abin mu ajiye ayoyin Alkur'ani mai girma da suka yi magana dangane da tsayin daka da kuma fada da zalunci da girman kai ne, to amma babban abin da ya faru na juyin mulkin ranar 28 ga watan Mordad 1332 kawai ya isa ya nuna mana yadda ya kamata mu yi mu'amala da Amurka.
A ci gaba da bayanin abin da ya faru a wancan lokacin mai muhimmancin gaske na ‘yan kasantar da kamfanin mai, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana yarda da Amurka da Dakta Mosaddiq (firayi ministan Iran na lokacin) a matsayin babbar kuskuren da ya aikata inda ya ce: Don fada da Ingila, Mosaddiq ya dogara da Amurka, a saboda haka irin fatan alheri da karamin tunani da gafala, su ne suka share fagen nasarar da wannan juyin mulki na Amurka ya samu. Juyin mulkin da ya mayar da dukkanin kokarin da mutane suka yi wajen ‘yan kasantar da kamfanin man fetur din ya zamanto aikin baban giwa. Ya sake rayar da lalatacciyar gwamnatin kama karya ta ‘ya'yan gidan sarautar Pahlawi da kuma sanya kasar Iran cikin mafi munin cutarwa ta siyasa da tattalin arziki da al'adu na tsawon shekaru 25.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin tasiri da fadi a ji da Amurka ta samu a Iran bayan juyin mulkin 29 ga watan Mordad din, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Wajen tinkarar irin wadannan yanayin, al'ummomin da ba su da shugabannin da suka dace, nan take suke mika kai. To amma al'ummar Iran ta hanyar amfanuwa da kyautar Allah ta jagorancin marigayi Imam Khumaini, sai ya zamana a kullum sai kara fadaka da fahimta suke yi, sannan kuma ta hanyar yunkuri na Musulunci suka sami nasarar kawar da hukumar ‘yan amshin shata ta Pahlawi da kuma babbar mai daure mata gindi.
Har ila yau kuma yayin da yake ishara da jawabin marigayi Imam Khumaini, yardar Allah ta tabbata a gare shi, a shekarar 1342 dangane da irin tsananin kiyayya da kyamar da al'ummar Iran suke nunawa shugaban kasar Amurka, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewar: tun ranar farkon kafa wannan yunkurin, wannan tsayayyen Jagora wanda yayi imani da alkawarin Ubangiji, ya gaya wa mutane cewa duk wani ashararanci da makirci, a bincike hannun Amurka a ciki.
Jagoran ya bayyana cewa kiyayyar Amurka da juyin juya halin Musulunci ta faro ne tun daga watannin farko-farko na nasarar juyin juya halin Musuluncin inda ya ce: Bayan nasarar juyin juya hali, har zuwa wani lokaci Amurkawa suna da ofishin jakadanci a Iran da kuma alaka da gwamnatin Iran. To amma koda da rana guda ba su daina kulla makirci ba. To wanann yanayin ya kamata ya zamanto abin da zai fahimtar da wasu cewa alaka da kuma abokantaka ba lamari ne da zai sanya Amurka ta daina makirci da kuma nuna kiyayya ba.
Ayatullah Khamenei ya bayyana kame ofishin jakadancin Amurka da wasu daliban jami'a na Iran suka yi a matsayin mayar da martani ga ci gaba da makircin Amurka da kuma mafakar da Amurka ta ba wa babban makiyin al'ummar Iran, wato Muhammad Ridha Pahlawi a kasar, don haka sai ya ce: takardun da aka samu a ofishin jakadancin Amurka suna nuni da cewa a hakikanin gaskiya ofishin jakadancin Amurkan ya zamanto wata sheka ce ta leken asiri sannan kuma wata cibiya ce ta kulla makirci wa al'ummar Iran da kuma juyin juya halin Musulunci.
Jagoran ya bayyana dubi da tuntuni cikin takardu da bayanan da aka samu a ofishin jakadancin Amurkan a matsayin wani lamari mai muhimmanci don daukar darasi. Daga nan sai ya ce: Wadannan takardun a fili suna nuni da cewa tun farkon kafa wannan yunkuri da ma bayan nasarar juyin juya hali, Amurka ta yi iyakacin kokarinta wajen cutar da al'ummar Iran.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da abubuwan da tsohon janar din Amurka wato Janar Huyser ya rubuta cikin littafin tarihin rayuwarsa na yadda ya zo Iran da nufin tseratar da gwamnatin Shah ta wancan lokacin, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Wannan abin a fili yana nuni da cewa Amurkawa suna kwadaitarwa da kuma shiryar da janar-janar na gwamnatin Shah wajen ci gaba da kashe al'ummar Iran.
Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da irin makice-makircen da Amurka ta kulla wajen raba kasar Iran da kuma cutar da juyin juya halin Musulunci da suka hada da juyin mulkin da ake kira da juyin mulkin Nojeh, kwadaitar da Saddam wajen kawo wa Iran hari da kuma taimakon da suka ce gaba da ba wa Saddam din tsawon shekaru 8 na kallafaffen yaki, a matsayin wasu bangare na irin makirce-makircen da Amurka take kulla wa Amurka.
Jagoran ya bayyana cewar: Amurkawa sakamakon rashin fahimtar hakikanin Iran, tsawon wadannan shekaru 37 na baya bayan nan sun yi ta kokari wajen rusa juyin juya halin Musulunci. Amma cikin yardar Allah sun sha kashi. Kuma a nan gaba za su ci gaba da shan kashin.
Ayatullah Khamenei ya bayyana cewa manufar sake dubi da kuma magana kan irin wadannan makirce-makirce na Amurka, ita ce kara fahimtar Amurkan da kyau. Daga nan sai ya ce: Cikin shekarun baya-bayan nan, akwai wasu mutanen da saboda cimma wata manufa ko kuma saboda karamin tunani suke ta kokari kyautata bakar fuskar Amurka da kuma nuna cewa idan har a baya Amurka ta kasance abokiyar gabar Iran, to a yanzu kan sun daina wannan makircin.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Manufar wannan kokari, ita ce kawar da irin wannan siffa ta kiyayya ta Amurka daga zukatan mutane, don Amurka ta sami damar ci gaba da wannan makirci nata, sannan kuma a duk lokacin da ta sami damar ta cutar.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Hakikanin lamarin shi ne cewa Amurka ba ta sauya manufarta a kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba. Don kuwa idan har za su iya kawar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran to kuwa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen yin hakan; to amma ba za su iya ba. Cikin taimakon Allah sannan kuma karkashin himma da kokarin matasa da kuma basirar al'ummar Iran, a nan gaba ma ba za su cimma wannan manufar ba.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da wasu alamu na sassauci na zahiri da jami'an Amurka suka nuna yayin tattaunawar nukiliyan da aka yi, Jagoran cewa yayi: Badinin wannan mu'amala ta Amurka, ita ce dai neman cimma wannan tsohuwar manufa ta adawa da gaba. To al'ummar Iran kuwa ba za ta taba mancewa da hakan ba.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: A yayin wannan tattaunawar daya daga cikin jami'an Amurka yayi magana kan irin kyamar yaki da yake da ita, kai hatta ma kuka yayi; mai yiyuwa ne wasu mutane masu karamin kwakwalwa su yarda da hakan. To amma irin goyon baya ido rufe da Amurka take ba wa azzaluman gwamnati masha jini ta sahyoniyawa da kuma goyon bayan da suke ba wa irin kisan gillan da ake yi wa mutanen Yemen, wani lamari ne da ke bayyanar da hakikanin wannan ikirari da kuma irin wannan kukan.
Har ila yau kuma yayin da yake ishara da alakar da Iran take da ita da kasashe daban-daban na duniya hatta ma da gwamnatocin da ba su da kyakkyawan manufa ga al'ummar Iran, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewar: Al'ummar Iran da irin wannan mahangar, ba za su taba ganin Amurka wacce take neman duk wata damar da za ta cutar da al'ummar Iran da ido na aboki ba, kuma ba za ta taba mika mata hannun abokantaka ba. Don kuwa shari'a ko hankali ko dan'adamtaka ba za su bar al'ummar Iran su aikata hakan ba.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da ci gaba da irin wadannan makirce-makircen da Amurka take aikatawa a kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Wadannan mutane sun fahimci cewa dalilin tsayin dakan al'ummar Iran shi ne imani da akida ta addini. A saboda haka ne a yau suke amfani da sabbin hanyoyi wajen fada da wannan akidar na addini. To amma (da yardar Allah) daliban makarantu, da na jami'oi da dukkanin matasanmu, za su mai da wannan makirci ya zamanto aikin baban giwa.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Makiya sun yi kokari daban daban wajen mayar da jami'oinmu su koma irin na zamanin lokacin Shah. To amma irin fadakar da matasanmu masu girma suke da ita ta sanya su riko da tafarki da koyarwar juyin juya hali. Lalle matasanmu za su kiyaye hakan.
Ayatullah Khamenei ya bayyana irin ci gaba da kuma karfin da al'ummar Iran suka yi a matsayin dalilin da ya tilasta wa makiya zama da Iran a teburi guda na tattaunawar nukiliya. Daga nan sai ya ce: Wadannan mutanen hatta a yayin tattaunawar ma sun yi amfani da irin wannan kiyayya ta su, ko za su sami damar dakatar da wannan yunkuri na ci gaba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar fahimtar irin kiyayya da makircin da Amurka take kullawa al'ummar Iran, ba wai hakan yana nufin rufe ido kan irin raunin da muke da shi ba ne. Daga nan sai ya ce: Muna da rauni a fagagen tsara siyasa da gudanarwa da kuma tsara abubuwan da ya dace a gabatar da su, wanda a mafi yawan lokuta makiya sun yi amfani da hakan.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: bai kamata mu yi kuskure wajen hada makiya da mutanen da muke da wani dan sabani da su ba. Shi makiyi shi ne wanda yake iyakacin kokarinsa wajen cutar da al'ummar Iran da kuma kawo wata gwamnati ‘yar amshin shata mai mika kai. To ta kowace fuska bai kamata a mance da irin wannan makiyin ba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: suka, wani lamari ne mai haifar da ci gaba. Don haka al'umma suna da hakkin yin suka, to amma bai kamata mu mance da wannan kalami na marigayi Imam Khumaini na cewa: "Duk wata la'anta da kuke da ita, ku yi ta kan Amurka".
A yayin da yake magana kan taken "Allah Ya La'anci Amurka" da da mahalarta taron suke ta rerawa, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Wannan take na la'antar Amurka da al'ummar Iran suke yi yana da tushe na hankali sannan kuma yayi daidai da kundin tsarin mulki da koyarwar wannan juyi wanda bai taba tafiya tare da zalunci ba.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Ma'anar wannan taken, ita ce la'antar siyasar Amurka da girman kanta, hakan kuwa wani abu ne da duk wata al'ummar da aka mata bayani za ta amince da shi.
A karshen jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Al'ummar Iran dai ta kuduri aniyar ci gaba da bin wannan tafarki da take kai, sannan kuma matasan yau za su ga wata rana da za ta zo da al'ummomi za su ‘yantu daga yanayi na tsoro, sannan kuma Iran za ta zamanto wata kasa mai karfafa sauran al'ummomi.
3439932