IQNA

An Nuna Kwafin Kur’ani Na Hubbaren Abbas A Bajen Kolin Duniya Na Bagdad

22:31 - November 09, 2015
Lambar Labari: 3446387
Bangaren kasa da kasa, an nuna wani kwafin kuerr’ani mai tsarki a baje kolin littafai na duniya da ake gudanarwa abirnin bagadaza fadar mulkin kasar Iraki.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na QAF cewa, wannan kwafin kur’ani mai tsarki mallakin hubbar Abbas Hamid Sa’adi ne ya rubuta wani mai fasahar rubutu dan kasar ta Iraki, wanda cibiyar buga littafai ta Darul Kafil ta buga.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan kwafin kur’ani mai tsarki ya ja hankulan mutane da dama  wajen wannan baje kolin littafai da yake gudana a birnin na bagadaza.

Wannan dai shi ne karon farko da cibiyar da ke kula da hubbaren Abbas (AS) ta dauki nauyin buga kur’ani mai tsarki ta wannan hanaya, inda marubucin Hamid Sa’adi ya rubuta shi da hannunsa, haka nan kuma n yi amfani da wani tsari na yanar gizo wajen saka alamomin da ke cikinsa.

Kwafin kur’anin mallakin hubbaren Abbas (AS) an buga shi ne bisa ruwayar Hafs bin Asem, wadda it ace ruwaya mafi shahara  akasar ta Iraki da ma sauran kasashen musulmi.

Karo na arbain da biyu Kenan da ake gudanar da wannan bababn baje kolin littafai na duniya a birnin bagadaza a kafa tun ranar 10 ga watan Aaban.

3446034

Abubuwan Da Ya Shafa: iraki
captcha