IQNA

Za A Gudanar da Gasar Kur’ani Ta Kasa Da Kasa Ta (Sayyid Junaid Alim) A Bahrain

22:32 - November 10, 2015
Lambar Labari: 3446871
Bangaren kasa da kasa, gasar wadda za a gudanar a karo na goma sha uku mai taken gasar Sayyid Junaid Ali za a fara gudanar da ta ne daga 21 ga watan Nuwamba zuwa 24.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «alayam.com» cewa, wannan gasa za a gudanar da ita tare da daukar nauyin masu hidima ga kur’ani mai tsarki na kasar da kuma cibiyar Sayyid Junaid Alim.

Cibiyar Muslunci ta Ahmad Al-fateh ita ce za ta dauki nauyin bayar da wurin d za  audanar da gasar, inda  ababban gininta za a hallara tare da makaranta da mahardata na kasashen duniya.

Abdulganiy Al-umary mamba  akwamitin da ke shirya gudanar da wannan gasa ya bayyana cewa, ko shakka babu masu hidima ga kur’ani mai tsarki sun bayar da gudumawa wajen shirya wanann gasa ta Sayyid Junaid.

Za daia  gudanar da gasar ne a bangarori biyu, da hakan yahada da bangaren karatu da kuma harda sai kuma bangaren kyautata karatu.

Al-uamri ya kara da cewa ya zuwa yanzu sun kamala dukaknin shirin da ya kamata domin gudanar da wannan gasa da kuma daukar nauyinta, kuma sun aike da goron gayyata ne zuwa kasashe ta hanyar ofisoshin jakadancinsu da ke kasar.

3446483

Abubuwan Da Ya Shafa: bahrain
captcha