IQNA

Mutumin Da Ke Yada Zanen Batunci Ga Manzo (SAW) A Danmark Ya Yi Murabus

22:48 - November 11, 2015
Lambar Labari: 3447350
Bangaren kasa da kasa, Felmin Roz mutumin da ke aiki da jaridar Yolandez Postin da ke yada zanen batunci kan manzo (SAW) ya yi ritaya daga aikinsa.


Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «ksalser.com» cewa, Felmin Roz dan jarida wanda ke aiki da jaridar Yolandez Postin a kasar danmark da ke yada zanen batunci kan manzo (SAW) ya yi ritaya daga aikinsa kamar yadda ya sanar.

Yawa wadannan zanen batuncin da yake yi kan ma’aiki da kuma addinin muslunci ya sanya ya fuskanci kakausar suka daga sassa na al’ummar kasar da ma kasashen ketare, da hakan ya hada har da cikin kasashen yammacin turai.

Marubucin y ace bisa la’akari da yanayin da yake ciki ya ajiye aikinsa, kuma a bhalin yanzu zai koma ne yin rubutu kawai kan lamaurra da suka danganci al’adu da kuma alaka a tsakanin al’ummomi, musamman na kasashen yammacin turai da yake rayuwa a ciki.

Tuna  cikin shekara ta 2005 ne dai ya fara yin wani rubtun batnci har sau 12 a cikin jaridar kan amnzo (SAW), wanda ya fuskanci kakausar suka daga alummomin duniya, wanda daga lokacin bai kara samun zaman lafiya, sakamakon irin barazanar da yake fuskanta a rayuwarsa.

Wanann mataki da ya dauka a halin yanzu dai yana da alaka ne da tsoron da yake ciki, kasantuwar cewa tun bayan lokaci bas hi da sukuni na yin walwala kamar sauran mutane, inda jami’an yan sanda ne suke binsa domin bas hi kariya.

3446990

Abubuwan Da Ya Shafa: danmark
captcha