IQNA

Hana Koyar Da Muslunci A Makantun Catholic Ya Saba Wa Sakon Paparoma

22:50 - November 11, 2015
Lambar Labari: 3447351
Bangaren kasa da kasa, Makarnatun majami’ar Catholic a kasar Birtaniya sun sanar da cewa za a daina koyar da wani bangare na addinai a makarantun kasar.


Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya hbarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Daily Mail cewa, a cikin sabon tsarin koyarwa na kasar Birtaniya, an bayar da umarni ga makarantun sakandare da kuma nag aba da su da su rika koyar da addini fiye da daya a tsarin koyarwa.

Amma duk da hakan makarnatun majami’ar Catholic a kasar ta Birtaniya sun sanar da cewa za a daina koyar da wani bangare na addinai a makarantun kasar domin hana yin aiki da wannan sabuwar doka ta ma’aikatar ilimi a bangaen tsarin koyarwa.

Jagororin musulmi  a kasar ta Birtaniya sun bayyan tuni makarantun da ke karkashin majami’ar Catholic suka fitar da tsarin koyar da darasin addinin mulsunci a cikin tsarin koyarwarsu.

Musulmin dai sun nuna rashin jin dadinsu dangane da wannan mataki da makarantun majamiar suka dauka, tare da bayyana cewa yana daidai da nuna banbaci ga musulmi a tsakanin al’ummomin kasar.

Wasu daga cikin masana suna kallon hakan a matsayin ya sabawa abin da babban shugaban majami’ar yake yin kira  akansa, na ganin cewa an samu fahimtar juna a tsakanin mabiya addinin kirista da sauran addinai musamman ma muslunci, inda yake karfafa koyar da wannan addini domin kiristoci su samu masani a kansa.

Yanzu haka dai majami’ar ta Catholic ta makarantu da yawansu ya kai 2000 a cikin sassa na kasar Birtaniya, wadanda suka hada da na sakandare da jami’oi gami da sauran kanan makarantu.

3446962

Abubuwan Da Ya Shafa: birtaniya
captcha