Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-arab cewa, ana gudanar da wannan aiki ne na gina massalatai a kasashen dubiya daban-daban, wanda cibiyar da ke gudanar da ayyukan alkhairi ta RAF karkashin Sheikh Thani bin Abdullah Qatar take gudanarwa a kasashen duniya.
Wadannan masallatai dai an gina su ne a cikin wasu akuyuka wadanda ba su da galihu, inda aka samar musu da wuraren karatu da kuma na kewayawa, gami da dakin masallacin wanda ake yi salla a cikinsa, baya ga wurin alwalla na musamman da aka samar.
3454520