Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «elkhabar.com» cewa, an kafa wannan kwamiti ne tare da hadin gwiwa atsakanin ma’aikatar kula da harkokin addinai ta kasar da kuma cibiyar jami’ar Amazigiya.
Muhammad Isa minister mai kula da harkokin addini a kasar Algeriya ya bayyana cewa, an kafa wannan kwamiti da nufin karfafa wannan aiki na rubuta tafsirin kur’ani mai a cikin wannan dadadden harshe.
Ya ci gaba da cewa wannan aiki ne da yake da matukar muhimmanci, domin kuwa zai taimaka wajen kara habbaka wannan yare ta fuskar addini da kuma fassara akr’ani mai tsarki wanda shi ne littafi mafi girma da tsarki a wajen ma’abota harshen.
Harshen Amazigi ko kuma Barbar shi ne harshen da ake Magana da shi a wasu kasashen Afirka kamar Morocco da Algeriya kafin larabci, sai kuma kasashen Libya da Tunisia da Mali a wasu bangarorinsu kadana ana Magana da shi.
3454708