IQNA

Kawancen Kasashen Turai Masu Da’awar Yaki Da Ta’addanci Ba Abin Dogara Ba Ne

21:07 - November 23, 2015
Lambar Labari: 3456301
Bangaren siyasa, jagoran juyin juya hali a lokacin da yake ganawa da shugaban Najeriya ya bayyana cewa, kasashen turai da ke da’awar yaki da ta’addanci baa bin dogara ba ne.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jagora na yanar gizo cewa, da hantsin yau Litinin ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari wanda ya kai masa ziyarar ban girma a gidansa da ke nan Tehran.

A jawabin da ya gabatar yayin ganawar, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana karfafa alakar da ke tsakanin kasashen Musulunci wajen kare matsayi da mutumci na Musulunci da musulmi a matsayin wani al'amari da ya zama wajibi, daga nan sai ya ce: Koda wasa hadin gwiwan kasashen duniya masu da'awar fada da kungiyoyin ‘yan ta'adda ba abin dogaro ba ne, don kuwa su kansu wadannan kasashen irin su Amurka su ne suka samar da kuma goyon bayan irin wadannan kungiyoyin na ta'addanci irin su Da'esh (ISIS).

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar "makiyan Musulunci na fili" da kuma "makiyan da suke nuna adawarsu ga Musulunci da sunan Musulunci" Danjuma da Danjummai ne, don haka sai ya ce: Don fada da wadannan makiya masu hatsarin gaske, wajibi ne kasashen musulmi su kara karfafa alakar dake tsakaninsu da kuma kiyaye manufofinsu.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar dogaro da taimakon Amurka da kasashen yammaci wajen fada da kungiyoyin ‘yan ta'adda irin su Da'esh da Boko Haram wani kuskure ne mai girman gaske, daga nan sai ya ce: Bisa ga ingantattun bayanai, Amurka da wasu kasashen yankin nan da suka ci baya su ne suke taimakon kungiyar Da'esh kai tsaye a kasar Iraki da kuma taka rawa wajen rusa kasar.

Jagoran ya bayyana cewar karfafa alaka tsakanin kasashen musulmi ba yana nufin toshe kofar alaka da sauran kasashen duniya ba ne, don haka sai ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da kyakkyawar alaka da dukkanin kasashe in ban da Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila, to amma mun yi amanna da cewa wajibi ne kasashen musulmi su ci gaba da karfafa alakar da ke tsakaninsu.

Har ila yau kuma yayin da yake bayyana farin cikinsa dangane da zaban shugaba Buhari da aka yi a matsayin shugaban kasar Nijeriya kana kuma mutum mai riko da koyarwar Musulunci, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar akwai fagage masu yawa da kasashen biyu za su iya karfafa alakar da ke tsakaninsu. Jagoran ya kara da cewa: Wajibi ne a gano wadannan fagage sannan kuma a yi amfani da su.

Shi ma a nasa bangaren, shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya, wanda mataimakin shugaban kasar Iran Malam Ishaq Jahangiri ke wa jagoranci, ya bayyana alakar da ke tsakanin Iran da Nijeriya a matsayin wata alaka mai karfin gaske, yana mai cewa: Iran kasa ce mai girma wacce kuma ta ci gaba da kuma fagage masu yawa da za a iya aiki tare da ita.

Har ila yau kuma yayin da yake jinjinawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan daukar bakuncin wannan taro na kasashe masu arzikin man fetur na duniya, shugaba Buhari ya bayyana cewar: Lalle na dau darussa masu yawan gaske albarkacin wannan ganawa da na yi da Jagoran juyin juya halin Musulunci. Lalle na ji dadin ganawar da kuma irin nasihohin da na ji.

3456070

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha