Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa Vladimir Putin a yayin ganawa da jagora tare da tawagarsa ya mika kyautar kwafin kur’ani mai tsarki ga jagoran.
Bayan kammala ganawarsu ne a jiya shugaban na Rasha ya mika wannan kur’ani da aka rubuta da hannu ga jagoran.
Abubwan Da Ku’anin Da Putin Ya Mika Wa Jagora Ya Kebantu Da Su
Rubutun wannan kur’ani da shugaban na Rasha ya bayar kyauta ga jagoran juyin juya hali yana komawa ne zuwa lokacin Marwan sarki na karashe a daular Bani Umayyah, wanda daga bisani ya isa hannun wani sarki daular Usmaniyya, wanda shi kuma ya bayar da shi ga sarkin Kajariyawa, daga nan kuma Naib Sultan ya bayar da shi ga Rashawa a lokacin yakin da aka yi tsakaninsu da Kajar, bayan da suka muslunta.
Ana a jiye wannan kwafin kur’ani mai tsarki da aka rubuta da hannu ne tsawon shekaru a wani dakin tarihin da ke kasar Rasha.