IQNA

Kasashen Musulmi Masu Fahimtar Za Su Iya Yin Aiki Tare wajen Yaki Da Ta’addanci

21:05 - November 25, 2015
Lambar Labari: 3457204
Bangaren siyasa, jagoran juyin juya hali a lokacin da yake ganawa da firayi ministan kasar Algeriya ya bayyana cewa kasashen da suke da fahimtar juna za su iya yin aiki tare domin yaki da ta’addanci.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto tarjamar rahoton daga shafin jagora kamar hakar, a hantsin yau Talata ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da firayi ministan kasar Aljeriya Abdulmalik Selal da ‘yan tawagarsa da suka kawo wa Jagoran ziyarar ban girma a gidansa da ke birnin Tehran, inda yayin da yake ishara da irin kusacin mahanga ta siyasa da ake samu tsakanin Iran da kasar Aljeriya ya bayyana cewar: Baya ga kusacin mahanga ta siyasa, a koda yaushe al'ummar Iran suna kallon al'ummar kasar Aljeriya kallo na so da kauna. Hakan kuwa ya samo asali ne sakamakon tsayin dakan al'ummar Aljeriya wajen tinkarar ‘yan mulkin mallaka a lokacin juyin juya halin kasar Aljeriyan.

Jagoran ya bayyana alaka ta ruhi da zuci da ke tsakanin al'ummomi a matsayin wani fage mai kyaun gaske na fadada alaka musamman a fage na tattalin arziki. Daga nan sai ya ce: Alaka ta tattalin arziki da ke tsakanin Iran da Aljeriya tana a matsayi na kasa kasa. Don haka muna fatan, wannan ziyarar da kuma kafa kwamitin hadin gwiwa, da kuma ziyarar ziyarar Malam Jahangiri zuwa Aljeriya, hakan zai zamanto wani share fage karfafa alaka ta tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da maganganun firayi ministan kasar Aljeriya dangane da matsalar kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh da kuma wajibcin fada da ‘yan ta'adda da suke shafa kashin kaji ga addinin Musulunci, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Batun Da'esh da kuma ‘yan ta'addan da suka yadu a yankin nan da sunan Musulunci, ba wai wani lamari ne karami ba, face dai wadannan ‘yan ta'adda an samar da su ne da kuma ci gaba da goyon bayansu.

Har ila yau kuma yayin da yake nuna bacin ransa kan yadda wasu kasashen musulmin yankin Gabas ta tsakiya suke goyon baya da taimakon kungiyar Da'esh, haka nan kuma da irin taimakon da Amurka da sauran makiyan Musulunci suke ba wa wannan kungiyar ta ta'addanci, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: kasashen musulmi masu kishi wadanda suke da alaka mai kyau a tsakaninsu, za su iya tattaunawa da junansu wajen gano hanyar da ta dace wajen fada da wadannan ‘yan ta'addan.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan kungiyar ‘yan gwagwarmaya da ta hada da Aljeriya, Iran, Siriya da wasu kasashe na daban da aka kafa tun farko-farkon nasarar juyin juya halin Musulunci, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Wasu kasashen da suka zamanto ‘yan amshin shatan Amurka, sun yi kafar ungulun ci gaban wanzuwar wannan kungiyar. To amma daga dukkan alamu a halin yanzu akwai fagen sake kafa irin wannan kungiya da za ta hada kasashen musulmi da suke da mahanga iri guda.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Idan har aka kafa irin wannan kungiyar, to kuwa wadannan kasashen za su iya yin tasiri cikin batutuwa masu muhimmanci na duniyar musulmi da kuma aikata wani abu a kas wajen fada da ‘yan ta'adda.

Daga karshe Ayatullah Khamenei ya bayyana fatan Allah ya gaggauta ba wa shugaban kasar Aljeriyan Abdel'aziz Bouteflika sauki.

Shi ma a nasa bangaren, firayi ministan kasar Aljeriya Abdulmalik Selal, wanda mataimakin shugaban kasar Iran Eshaq Jahangiri yake wa jagoranci, ya bayyana taron shugabannin kasashe masu arzikin iskar gas da aka gudanar a matsayin wani taro da aka samu nasarori a cikinsa, sannan kuma yayin da yake ishara da tattaunawar da yayi da jami'an kasar Iran ya bayyana cewar: mahangar kasashen Iran da Aljeriya musamman cikin batutuwan da suka hada da fada da kungiyar Da'esh da sauran ‘yan ta'addan da suke yankin nan mahanga ce da ta yi da kama da juna. A saboda haka ina fatan bisa la'akari da tattaunawar da muka yi, za a karfafa alakar tattalin arziki da ke tsakanin kasashen biyu.

3456543

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha