Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar Imam Ali (AS) cewa, Jonathan Steel tsohon dan jaridar Guardian ta kasar Birtabniya a lokacin ganawarsa da shugaban cibiyar kula da hubbaren Imam Ali (AS) Nazar Hashim Hablul matin ya bayyana cewa sanin tarihim Imam Ali (AS) ya yi amfani maras misiltuwa a cikin rayuwarsa baki daya.
Steel y ace zuwansa wannan wuri domin ya san tarihin Imam Ali da kuma falsafar hubbarensa, ya zama wani abu mai matukar kima da matsayi a wurinsa.
Ya ce shugaban cibiyar Hubbaren Imam Ali (AS) ya yi masa gamsashen bayani kan tarihi wannan wuri mai matsayi.
3457273