IQNA

An Gudanar Da Tarukan Arbaeen Na Imam Hussain (AS) tare Da Halartar Jagoran Juyi

23:45 - December 03, 2015
Lambar Labari: 3459637
Bangaren siyasa, an gudanar da taron arbaeen tare da halartar jagoran juyin juya halin muslunci da sauran jami’a.


Kamfanin dilalncin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa nayanar gizo na ofishin jagora cewa, a yau Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei jagoran juyin ya halarci taron arbaeen na Imam Hussain (AS) a Hussainiyar Imam Khomenei (RA)

Haka nan kuma miliyoyin al’ummar Iran ne suka fito kan tituna da Husaniyoyi da masallatai, duk kuwa da ruwan saman da ake yi a yankuna daban-daban na kasar, a yau din nan Laraba don gudanar da bukukuwan juyayin arba’in na shahadar Imam Husain (a.s).

Kamfanin dillancin labaran Iran ya bayyana cewar tun da safiyar yau din nan ne da miliyoyin mutanen birnin Tehran, babban birnin kasar ta Iran, suka fito kan tituna da wajajen tarurruka suna masu rera taken nuna goyon bayansu ga iyalan gidan Manzon Allah da kuma Allah wadai da makiyansu.

Har ila yau a nan Tehran din dai Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jagorancin taron juyayin Arba’in din da aka gudanar a Husainiyar Imam Khumaini (r.a) da ke gidansa, da ya sami halartar manyan jami’an kasar da sauran al’ummar birnin na Tehran.

Rahotanni daga sauran garuruwa na kasar ma dai suna nuni da cewa miliyoyin masoya Ahlulbaiti (a.s) ne suka fito cikin tufafi na juyayi suna rera wakokin juyayin ranar.

3459345

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha