Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nun cewa, Jamil Zahiri jagoran gudanar da shirin na cibiyar Zul-fiqhar ya bayyana cewa, dubban masu tafiya zuwa ziyarar arbain na Imam Hussain sun rubuta kur’ani mai tsarki a kan hanyarsu ta isa hubbarensa mai tsarki da ke birnin karbala mai alfarma.
Inda sukan tsaya domin rubuta abin da ya sawaka na daga ayoyin kur’ani gewargwadon yadda suke da shawar yin hakan kamar dai yadda bayanin ya nuni da hakan, kuma haka nana gudanar da shi ne bisa zabin masu ziyarar.
Wadanda suka gudanar da ziyarar arbaeen ta wannan shekara dai adadinsu ya haura dukkanin shekarun da suka gaba, domin kuwa fiye da mutane miliyan ashirin da shida ne suka gudanar da ayykan ziyarar a wannan shekara.
Ya ci gaba da cewa an samu dubban mutane da suka shiga cikin wannan shirin, kamar yadda kuma an bayar da dama ga masu ziyarar su rubuta wani abu gwagwardon yadda za su iya, duk kuwa da cewa an yi la’akari da yawan mutane domin bayar da dama ga wasu masu shawa su samu.
3459675