IQNA

Iran Ta Yaba Wa Iraki Dangane Da Gudanar Da Tarukan Arbaeen Cikin Nasara

23:20 - December 06, 2015
Lambar Labari: 3460516
Bangaren kasa da kasa, ofishin jakadancin Iran a Bagdad ya yaba da yadda aka gudanar da tarukan arbaeen cikin nasara a Iraki.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alfurat News cewa, ofishin ofishin jakadancin jamhuriyar muslunci ta Iran ya yaba da yadda aka gudanar da tarukan arbaeen a hubbaren Imam Hussain (AS) cikin nasara a wannan shekara.

A nasu bangaren su ma dakarun sa-kai da suke taimakawa jami’an tsaron Iraki a fagen yaki da ta’addancin kungiyar Da’ish sun rusa wani babban makircin kai hare-haren bama-bamai a lokacin juyayin Arba’in na Imam Husaini {a.s}.

Babban sakataren dakarun sojin sa-kai na Sayyidul-Shuhada a kasar Iraki a hirarsa da tashar talabijin din a daren jiya Laraba ya sanar da cewa; Dakarun sa-kai da hadin gwiwar jami’an tsaron Iraki sun samu nasarar rusa wani gagarumin makircin kungiyar ta’addanci ta da’ish mai kafirta musulmi ta kai wasu jerin hare-haren kunan bakin wake kan taron jama’ar da suke gudanar da juyayin ranar Arba’in na jikan Manzon Allah Imam Husaini {a.s} a sassa daban daban na kasar Iraki da tarin motoci hamsin da takwas da suka makare su da bama-bamai.

Abu-A’la ya kara da cewa; Kungiyar ta’addanci ta da’ish ta shirya fara aiwatar da wannan mugun aniya nata ne da misalin karfe sha biyu na daren jiya Laraba, amma kafin lokacin dakarun sa-kai suka gano makircin tare da rusa shi baki daya.

3460471

Abubuwan Da Ya Shafa: iraki
captcha