IQNA

Jamus Ta Bukaci Saudiyya Da Ta Daina Daukar Nauyin Yada Tsatsauran Ra'ayi A Duniya

23:32 - December 07, 2015
Lambar Labari: 3460938
Bangaren kasa da kasa, mataimakin shugabar gwamnatin kasar Jamus ya bukaci kasar Saudiyya da ta daina daukar nauyin cibiyoyi masu yada tsatsauran ra’ayi.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Press TV cewa, Sigmar Gabriel Mataimakin shugabar gwamnatin Jamus ya bukaci Saudiyya da ta daina daukar nauyin masallatai masu yada tsatsauran ra'ayi a kasashen duniya.



Mataimakin shugabar gwamnatin Jamus Sigmar Gabriel ya bayyana cewa, ya zama wajibi kan gwamnatin Saudiyya da ta daina daukar nauyin masallatai da ke yada tsatsauran ra'ayi, inda ya ce masallatan da ke yada akidar wahabiyanci a duniya Saudiyya ce ke daukar nauyinsu, kuma daga nan ne ake samar da tsatsauran ra'ayi da ke haifar da 'yan ta'adda.



Mataimakin shugabar gwamnatin kasar ta Jamus wanda kuma shi ne ministan tattalin razikin kasar ya kara da cewa, dukkanin mutanen da suke da matukar hadari ga tsaron kasar Jamus sun fito daga wannan cibiya da take dauke da wannan akida ta wahabiyanci.



Sai dai a daya bangaren ya ce za su ci gaba da tattaunawa da Saudiyya dangane da rikicin kasar Syria, kasantuwar tana da tasiri kan masu tayar da kayar baya a kasar ta siriya da ke da'awar jihadi.



3460613

Abubuwan Da Ya Shafa: jamus
captcha