Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren adana bayanan jagora Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khameni cewa, hakikanin ma’anar kalamar rabi tana komawa ga watan Rabil Awwal.
Bayanin ya ce wannan wata mai albarka a ne aka haifi fiyayyen halitta manzon Rahama da kuma Imam Jafar sadiq, wanda kuma wadannan mutane biyu manzo da jikansa su ne misadkin sa’ada da rahama.
Wadanda suka yi nisa a cikin lamarin sanin ubangiji suna da masaniya kan matsayin wannan wata ta wasu fuskoki na irfani kasantuwar hakan yana da alaka ne da ilimi na boye a mafi yawan lokuta sabanin abin da yafi zama zahiri ga mutane.
Manzon Allah rahma ce ga dukaknin talikai kamar yadda Allah madaukakin sarki ya bayyana shi acikin kuran mai tsarki, tare da bayyana koyi da wannan manzo ita ce babbar hanyar isa ga sa’adar bangiji madakakin sarki.
An yi bayanin a lokacin ganawa da jami’ai da kuma bakin makon hadin kai 10-11-1391