Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga tashar Alalam cewa, rahotanni daga kasar Labanon sun bayyana cewar an sako dan tsohon shugaban kasar Libiya marigayi Kanar Mu'ammar Gaddafi, wato Hanibal Gaddafi, bayan da wasu mutane suka kama da kuma yin garkuwa da shi bayan da ya iso kasar ta Labanon.
Shi ma kamfanin dillancin labaran ya jiyo wata majiyar tsaron kasar ta Labanon tana fadin cewa 'yan sandan kasar Labanon din sun karbo Hanibal Gaddafi daga wajen mutanen da suka yi garkuwa da shi din a daren jiya, tana mai cewa jami'an tsaron za su gudanar da bincike kansa ba tare da ta yi karin bayani kan wadanda suka yi garkuwa da shi din ba.
A wata hira da yayi da gidan talabijin din Al-Jadeed ta kasar Labanon din, Hanibal Gaddafi ya bayyana cewar yana cikin koshin lafiya, kamar yadda kuma ya bayyana wadanda suka sace shi din a matsayin mutane masu tsoron Allah wadanda suka kyautata masa mu'amala, kamar yadda kuma ya bukaci duk wanda yake da wani bayani kan lamarin Imam Musa al-Sadr da ake zargin mahaifinsa da sace shi da ya fito ya fadi.
Ana zargin tsohon shugaba Gaddafi da sace Imam Musa al-Sadr, shugaban majalisar koli ta 'yan Shi'an kasar Labanon din a lokacin da ya kai ziyara kasar Libyan a shekarar sabain da takwas kuma har ya zuwa yanzu babu labarinsa.
Dan na Ghaddafi ya bayar da muhimman bayanai wadanda za su taimaka matuka wajen gudanar da bicike kan makomar Imam Musa Sadr wanda mahaifisa ya sace tare da hadin baki da wasu daga cikin kasashen larabawa tun kimanin shekaru fiye da talatin da bakawai da suka gabata.
Tun bayan sace Imam Musa Sadr har yanzu babu wani bayani dangane da makomarsa, duk kuwa da cewa kafin kashe gaddafi ya bayyana cewa ya fita daga kasar, amma dukkanin dalilai sun tabbatar da cewa baii fita kuma wasu daga cikin jami’an tsarosa da aka kama sun ce ya kashe shi.
Har yanzu dai ana ci gaba da bin dukkanin hanyoyin da suka kamata domin sanin makomarsa, da nufin gano hakikanin abin da ya faru da shi, kamar yadda kuma wasu majiyoyin suke cewa babu wata fata a ta samunsa a raye, domin baya ga bayanan da jami’an suke bayarwa, babu wani bayani mai karfafa gwiwa kan samunsa a raye daga gidajen kaso.
3463516