IQNA

Daliban Jami’a A Amurka Suna Yaki da Kyamar Musulmi

22:24 - December 15, 2015
Lambar Labari: 3463638
Bangaren kasa da kasa, daliban jami’a a cikin jahar Alabama wadanda ba musulmi ba ne sun bullo da wata hanya ta yaki da kymar mabiya addinin muslunci a kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «wvtm13» dalibai 60 suka kafa wannan kungiya wadda take wayar da sauran yan uwansu Amurka dangane da nisatar akidar nan ta kyamar musulmi.



Daliban suka duk da irin kyamar da ake nuna ma muslmi hakan ba zai hana su ci gaba da yin abin da suka sanya a gab aba na wayar da kan mutanen kasarsu danagne kiransu su daina kyamar musulmi.



Briana Braiden tana daga cikinsu, ta kuma bayyana cewa idan da a ce ita musulma ce hakan ba yana nufin kuma yar Daesh ce ba.



Bent Etgenz shi ma yana da cikin wadannan dalibai, inda ya bayyana cewa akwai musulmi fiye da biliyan daya  aduniya, hakan bayana nufin cewawasu yan tsiraru yan ta’adda suna wikiltarsu ba ne baki daya.



Rebca Hartaclas tana daga cikin daliban wadda ta bayyana cewa babbar manufarsu it ace samar da danganta a tsakanin mutanen Amurka da kuma marassa rinjaye a kasar musamman ma muslmi da ake kyamata.



Sun bayyana cewa a shirye suke su ci gaba da gudanar da wannan aiki wanda yake nay an adamtaka ne, kuma suna da imamin cewa za su yi nasara wajen wajen wayar da kan wasu ko da kwa wasu ba a masa ba wasu za su amshi nasiharsu.



Tun bayan hare-haren ta’addanci daka kai a cikin yan watannin a  cikin wasu daga cikin kasashen turai, kayamatar musulmi ta karu mtuka a cikin kasashen turai musamman ma a kasar Amurka.



3463452

Abubuwan Da Ya Shafa: amurka
captcha