IQNA

Kokarin Wanke Kawancen Saudiyya Ta Fuskar Fikhu

23:14 - December 18, 2015
Lambar Labari: 3465573
Bangaren kasa da kasa, bayan da Suadiyya ta kafa kawancen da ta kira na yaki da ta’addanci na kasashen musumi cibiyar fikihu ta duniya tana kokarin samar da hujjoji domin domin tabbatar da abin da saudiyya ta yi.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alalam cewa, cibiyar fikihu ta duniya tana kokarin samar da hujjoji domin domin tabbatar da abin da saudiyya ta yi wanda ake shakku kan lamarin da kuma manufarsa.

Tun ba a je ko ina ba shirin kokarin wasa da hankalin al'umma don rufe irin goyon bayan da suke ba wa kungiyoyin 'yan ta'adda da kasar Saudiyya ta shigo da shi ta hanyar sanar da kafa wata hadaka ta dakarun sojin kasashen musulmi da nufin abin da suka kira 'fada da ta'addanci', shirin ya fara fuskantar koma baya bayan da wasu kasashen da aka ce suna cikin hadakar suka sanar da cewa su ba su da wani labari kan hadakar.



Kwana guda bayan da Muhammad bn Salman, dan sarkin Saudiyyan kuma ministan tsaro sannan kuma yariman yarima mai jiran gadon kasar Saudiyya, ya sanar da kafa hadakar kasashe 34 don fada da ta'addanci karkashin jagorancin kasar Saudiyyan, wasu kasashen da aka ce suna ciki din irin su Labanon da Pakistan suka sanar da cewa su ba a tuntube su ba kuma ba su da wata masaniya kan hakan, don haka suka bukaci kasar Saudiyya da ta musu karin bayani kan wannan lamarin.



A nata bangaren ma'aikatar harkokin wajen kasar Labanon, cikin wata sanarwa da ta fitar, ta yi kakkausar suka ga wannan sanarwar ta ministan tsaron naSaudiyya na cewa kasar Labanon tana cikin hadakar amma ba tare da an sanar da ita ba inda ta ce kasar Labanon tana adawa da duk wani abin da zai raunana matsayin kasar da kuma nauyin da ke wuyanta a fagen kasa da kasa.



Ita ma a nata bangaren gwamnatin kasar Pakistan, ta bakin mataimakin ministan harkokin wajen kasar Aizaz Ahmad Chaudary ya bayyana wa manema labarai tsananin mamakinsa dangane da sanarwar cewa Pakistan tana cikin hadakar yana mai cewa kasarsa ba ta da wannan labarin.



A ranar Litinin din da ta gabata ne, ministan tsaron Saudiyyan Muhammad bn Salman ya sanar da kafa abin da ya kira 'hadakar kasashe 34 da nufin fada da ta'addanci' karkashin jagorancin kasar Saudiyya. To sai dai kuma tun a lokacin, tun ma kafin wasu kasashen da aka sanya sunayen na su su fara nuna rashin amincewarsu, wasu suka fara sanya alamun tambaya kan manufar hadakar da kuma yiyuwar cimma nasararta, suna masu cewa wani irin hadaka ta kasashen musulmi ne za a kafa amma kuma wasu manyan kasashen musulmin irin su Aljeriya, Afghanistan, Iran, Iraki da Siriya, wadanda mafi yawansu ma suna fuskantar ta'addancin kai tsaye amma ba sa ciki.

Wani abin da ke kara sanya shakku cikin manufar Saudiyya kan kafa wannan hadakar shi ne cewa a daidai lokacin da Saudiyyan take sanar da kafa hadakar fada da ta'addancin, amma gwamnatocin kasashe irin su Iraki da Siriya wadanda suka zamanto tungar 'yan ta'addan a halin yanzu suna zargin kasar Saudiyya, tare da hadin gwiwan kasashe irin su Qatar da Turkiyya, wadanda su ma suna cikin hadakar, a matsayin kasashen da suke kan gaba wajen goyon bayan ayyukan ta'addancin da ke faruwa a yankin Gabas ta tsakiya musamman a kasashen Iraki da Siriya.



A saboda haka ne da dama daga cikin masana da masu fashin bakin magana suke ganin manufar kafa wannan hadakar karkashin jagorancin Saudiyya ita ce kokarin rarraba kan al'ummar yankin bisa tushen kabilanci da mazhaba da kuma rufe irin danyen aikin da Saudiyya take yi na kirkirowa da kuma goyon bayan kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin Gabas ta tsakiya da ma sauran yankuna na duniya wadanda a halin yanzu suka fara zama karfen kafa hatta ga kasashen yammaci.



Jaridar kasar Amurka ta bayyana shirin gwamnatin Saudiyya na kafa abin da ta kira hadakar kasashe 34 don fada da ta'addanci a matsayi wani kokari da gwamnatin Saudiyya take yi na neman yardar Amurka da kuma yaudarar kasashen Yammaci.



Kafar watsa labaran -Ahad ta kasar Labanon ta bayyana cewa a yayin da take sharhi kan sanarwar da gwamnatin Saudiyyan ta yi na kafa hadakar sojojin kasashe talatin da hudu da nufin fada da ta'addanci a duniya, Jaridar ta bayyana cewar manufar kafa wannan hadakar ita ce cimma manufofin Saudiyya na rarraba kan al'umma da sunan goyon bayan kasashen 'yan Sunna da kuma kokari wajen yaudarar kasashen yammaci.



Jaridar ta kara da cewa sakamakon kakkausar suka da kasashen Yammaci suke yi wa gwamnatin Saudiyya wajen goyon bayan ayyukan ta'addanci ko kuma alal akalla rashin tabuka komai wajen fada da yaduwar tsaurin ra'ayi, hakan ne ya sanya Saudiyyan kirkiro wannan hadakar don cimma manufarta da kuma neman yardar Amurka.



A ranar Litinin din da ta gabata ce, ministan tsaron Saudiyyan Muhammad bn Salman ya sanar da kafa abin da ya kira 'hadakar kasashe talatin da hudu da nufin fada da ta'addanci' karkashin jagorancin kasar Saudiyya; lamarin da tun ba a je ko ina wasu daga cikin kasashen da aka sanya su cikin hadakar suka nuna rashin amincewarsu da hakan.



3464418

Abubuwan Da Ya Shafa: saudiyyah
captcha