Kamfanin dillancin labaran Iqna nay a nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dilalncin kasar Mauritaniya ya bayar da rahoton cewa, an bude taron ne abirnin Nuwakshout fadar mulkin kasar, kasar tare da halartar malamai da masana daga ciki da kuma wajen kasar, wanda zai kwashe tsawon kwanaki uku ana gudanarwa.
Wannan dai shi ne karo na ashirin da shida da ake gudanar da wannan taro, wanda kuma yake zuwa daidai lokacin gudanar da tarukan maulidin manzon Allah, kuma daga cikin kasashen da suke samun halartarsa akwai Morocco, Tunisia, Senegal, Turkiya, Nijar, Gambia, da Saudiyya.
Ahmad Wuld Ahl Dawud shi ne ministan ilimi na kasar, ya bayyana a wajen bude taron cewa, matsayin manzon Allah (SAW) lamari ne mai girma, kamar yadda Allah ya bayyana hakan a cikin kur'ani mai tsarki.
Ministan Iilimin na Murtaniya ya ce matsayin manzon Allah da soyayyarsa a cikin zukatan muminai tana da alaka ne da koyarwarsa.
Ahmad Wuld Ahl Dawud ya kara da cewa ana gudaar da wannan taro ne tare da taimakon cibiyar yada al'adu da kuma wasu bangarori na kundiyoyin addinia yammacin nahiyar Afirka, domin raya matsayin manzon Allah (SAW) da koyarwar kur'ani.
Manyan jami'an gwamnati sun samu halartar taron, da suka hada da mai bayar da shawar ga shugaban kasa kan harkokin addini, dakuma wasu daga cikin jami'an diplomasiyya na kasashne musulmi.
3468092