IQNA

Isra’ila Ce Ta Kashe Samir Qentar / Hannun Yahudawa A Kisan Shi’a A Najeriya

22:32 - December 22, 2015
Lambar Labari: 3468424
Bangaren kasa da kasa, Sayyid Nasrulla babban sakataren Hizbullah ya yi bayani mai muhimmanci dangane da kisan Qentar.


Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo na tashar Alalam cewa, a jawabin sa jagoran kungiyar Hizbullah sayyid Hassan Nasrullah ya gabatar kan shadar Samir Qentar ya bayani mai muhimmanci matuka.



Sayyid Nasrullah ya mika sakon taya muna ga dukkanin mabiya addinin mirista da kuma muslulmi dangane da zagayowar lokacin haihuwar annabi Isa Almasih (AS) da kuma manzon Allah (SAW) a wannan lokaci.

Baya ga Sayyid Nasrullah, shahadar Samir Qantar daya daga cikin komandojin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon a kasar Syria ya gamu da maida martani da dama a kasar Lebanon da kuma sauran kasashen yankin.

Samir Qantar dais hi ne dan kasar Lebanon wanda yake dadewa a cikin kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila, inda a lokacinda yake dan shekara sha shida a duniya ya fada hannun yahudawan, sannan bayan ya share shekaru talatin a tsare, ya fi tare da taimakon kungiyar ta hizbullah inda ta yi musayarsa da wasu gawakin yahudawan da suke hannunta a shekara ta 2008.

A jiya asabar ne jirgin yakin haramtacciyar kasar Isra’ila ta keta hurumin sararin samaniyar kasar Syria ta jefa makamai a kan anguwar Jurmana dake kudancin birnin Damascus inda mutane da dama suka rasa rayukansu wasu kuma suka ji rauni . daga cikin su samir qantar.

A cikin kasar Lebanon dai yan siyasa da malaman addini da dama suka yi Allawadai da kisan suka kuma mika ta’aziyarsu ga kungiyar Hizbullah.

Shugaban binciken harshen larabci da kasa da kasa ya ce kungiyar hizbullah tana da hakkin maida martani kan kissan Samir qantar, sanna shahadarsa ya tabbatar mana cewa daurin da ya sha a cikin mafi yawan rayuwarsa bai sanya shi jada baya a kan manufarsa ta kasarsa da kuma Palasdinu sun sami enci daga hannun yahudawan da suke mamaye da su ba.

Shugaban wata jam’iyyar siyasa gurguzu ta kasar Lebanon ya mika ta’aziyyarsa ga shugaban kungyar hizbullah ta kasar sayyeed Hassan nasarallah. Ya kuma ce Samir qantar kekyewar masala ne na mujahidin wanda baya daddara cikin gwagwarmaya da ya sa a gaba.

Kungiyoyin Palasdunin sun yi Ala wadai da kisan Qantar sun kama bayyan cewa kungiyoyin masu gwagwarmaya sune da nasara a nan gaba.

Kakakin hamsa ya ce yahudawan sahyoyin suna bin dukkan majahidai inda suke don ganin bayansu. Kungiyar Fatah ta mahmod Abbas ta yi Allawadai da kisan qantar.

Sannan a nan jamhuriyar muslunci ta kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar usain jabiri Ansari yay i Alawadai da kisan Samir qantar, a cikin kasar Syria daya ne daga cikin rashin mutunta dokokin kasa da kasa wanda haramtacciyar kasar Isra’ila ta dade tana yi don kawo karshen kungiyoyi masu neman encin.

Wannan kuma ya tabbatar da cewa haramtacciyar kasar Isra’ila kasashe ta yan ta’adda wacce kuma take marawa yan ta’adda a kasashen duniya da dama don cimma mummunan manufofinta na mamayar kasashen musulmi da larabawa.



3468010

Abubuwan Da Ya Shafa: Hizbollah
captcha