IQNA

An Gudanar Da Jerin Gwanon Allawadai Da KIsan Musulmi A Najeriya

21:22 - December 25, 2015
Lambar Labari: 3469179
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da jerin gwano a biranan Najeriya domin yin Allawadai da nuna rashin amincewa da kisan gillan da sojoji suka yi kan musulmi.

Kamfanin dillancin labaran Iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Press TV cewa, ya nakalto da Associated Press cewa, dubban musulmin sun gudanar da zanga-zanga a biranan Najeriya domin nuna rashin amincewa da kisan da aka yi musulmi a Zaria.

 

Abdulhamid Bello ya gabatar da jawabi a gaban dubban mutane da suka taru suna yin Allawadai da hakan, wanda kuma ko shakka babu hakan ya dauki hankulan al’ummomin duniya tare da doora alhakin abin da ya faru kan rundunar sojin Najeriya na kisa da kama sheik Zakzaky.

Rahotannin daga Nijeriya sun bayyana cewar dubun dubatan 'yan kungiyar harkar Musulunci a Sokoto da Katsina da ke kasar sun fito kan tituna da dama daga cikin biranen kasa a yau Jumu'a don kiran mahukuntan Nijeriya da su sako jagoran kungiyar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da suka kama a ranar Litinin din da ta gabata.

 

Shafin harkar Musuluncin ya bayyana cewar an gudanar da irin wadannan jerin gwano da gangami ne a garuruwa daban-daban na kasar da suka hada da Katsina, Kano, Bauchi, Sakkwato, Jos, Jalingo, Suleja, Gombe, da sauran birane inda masu jerin gwanon wadanda suke dauke da hotunan Sheikh Ibrahim El-Zakzaky suka bukaci da a sako musu shugabansu da ke tsare a hannun jami'an tsaron kasar.

Shafin ya kara da cewa an dai gama jerin gwanon lafiya ba tare da faruwar wani rikici ba, har ya zuwa yanzu dai jami'an tsaron Nijeriyan suna ci gaba da tsare shugaban kungiyar 'yan'uwa musulmin a wani wajen da ba a tantance ko ina ba ne.

 

3469130

Abubuwan Da Ya Shafa: nigeria
captcha