IQNA

Amurka Ta Soke Izinin Shiga Cikin Kasarta Ga Limamin Birtaniya

21:27 - December 25, 2015
Lambar Labari: 3469183
Bangaren kasa da kasa, Amurka ta soke izinin shiga cikin kasarta ga Ajmal Masrur.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Press TV cewa, Ajmal Masrur daya daga cikin manyan limamai a kasar Birtaniya, Amurka ta soke izinin shiga ta bas hi ba tare da bayyana wani dalili kan yin hakan ba.

Ajmal Masrur dai yana da cikin fitattn limaman masallatan birnin London na kasar ta Birtaniya, kuma wannan bas hi ne karon farko da ya bukaci zuwa kasar Amurka, amma matakin hana shi visa ya saka alamar tambaya  akan cewa, ko kasar ta fara aiki da shawar Donald Trump ne, da ke neman a hana musulmi shiga cikin kasar.

An hana Masrur tafiya zuwa wani gari a cikin kasar Amurka da yake da niyar ganawa da wasu danginsa da suke zaune a can, duk kuwa da cewa jami’an kla da filin safka da tashin jiragen sama ba su yi masa wani Karin bayani ba kan hakan.

Jaridar Guardian ta bayar da rahoton cewa takardun shiga kasar Amurka da yake dauke da sub a su da wata matsala ta fuskar doka, kamar yadda kuma ya riga ya shiga cikin kasar ne aka soke masa izinin shigar wanda aka ba shi.

Masrur ya nfin ganawa da limamin wani masallaci ne a birnin New York, tare da ganawa da wasu mutane daga cikin iyalansa, amma aka hana shi hakan.

Kafin wannan lokacin ma jami’an Amurka sun hana wasu iyalai musulmi da suka yi nufin tafiya kasar daga kasar Birtaniya ba tare da wani dalili ba.

3469086

Abubuwan Da Ya Shafa: amurka
captcha