IQNA

16:39 - January 06, 2016
Lambar Labari: 3480030

Rashin Amincewa da Matsayar kafofin Yada Labaran Pkistan kan Kisan Sheikh Nimr

Bangaren kasa da kasa, kwamitin jakadun kasashen larabawa a kasar Pakistan ya nuna rashin amincea da matsayar da jaridun kasar Pakistan suka dauka na bayar da labara kan kisan Sheikh Nimr da saudiyya ta yi.

Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Ummat da ake bugawa a Karachi cewa, kwamitin jakadun kasashen larabawa a kasar Pakistan sun nuna rashin gamsuwarsu matsayar da jaridun kasar suka dauka kan kisan Sheikh Nimr da saudiyya ta yi a cikin kwanakin nan.

Kwamitin ya ce kai hari kan ofisoshin jakdancin Saudiyya a Tehran da kuma Mashhad ba daidai ba ne kuma ya saba wa dukkanin kaidoji, kuma tozarci da wulakanci ne ga dukkanin kasashen larabawa.

Kafofin yada labarai na kasar Pakistan da suka hada da na gwamnati da kuma masu zaman kansu, tun bayan kisan Sheikh Nimr da masarautar saudiyya ta yi sun yi ta bada labara kan batun.

Mafi yawan kafofin yada labaran na Pakistan suna sukar gwamnatin Saudiyya kan wannan aiki na dabbanci da rashin lissafin da karya dokokin kasa da kasa da rashin sanin kimar dan adam da ta nuna cikin lamarin.

http://iqna.ir/fa/news/3465100


captcha