IQNA

Kawar Da Juyi Shi Ne Manufar Makiya / Ko Wadanda Ba Su Amince Da Jagoranci Ba Su Shiga Zabe

15:55 - January 10, 2016
Lambar Labari: 3480035
Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya hali a lokacin da yake gabatar da jawabi a jiya ya bayyana cewa: manufar makiya ita kawar da duk wani abu da yake da alaka da juyin Islama, tare da kawar da tunanin al’umma kan koyarwar wannan juyi wadda ta ginu a kan koyarwar addinin muslunci na hakika.

Kamfanin dillancin labaran Inqa ya nakalto daga shafin jagora cewa, a safiyar yau Asabar 09-01-2016 ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Ozma Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubun dubatan mutanen garin Qum don tunawa da zagayowar shekarar yunkurin 19 ga watan Dey na shekarar 1356 da mutanen Qum din suka yi wajen tinkarar gwamnatin kama karya ta Shah da kuma nuna goyon bayansu ga tafarkin malamai; inda yayin da yake jinjinawa wannan yunkuri mai cike da tarihi na 19 ga watan Dey na 1356 da mutane Qum din suka yi da kuma karin bayani kan dalilan da suka sanya juyin juya halin Musulunci na kasar Iran ya ci gaba da yanzuwa, ya bayyana cewar: Ana iya tabbatar da wanzuwar juyin juya hali, zaman lafiya da kwaniyar hankalin al'umma da kuma samun nasara a kan makirce-makircen makiya ne ta hanyar kasantuwar mutane a fage sannan kuma a lokacin da ya dace.

Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana mutanen garin na Qum a matsayin ja gaban wannan juyi na Musulunci na kasar Iran inda ya ce: Shekara da shekaru na gwagwarmaya da kuma jawaban marigayi Imam Khumaini (r.a) da kuma irin matsayi na maraja'ai da malaman addini dukkanin wadannan abubuwa sun share wa mutane fagen fada da gwamnatin zalunci ta Shah, wanda yunkurin 19 ga watan Dey ya zamanto wani koli na wannan gwagwarmayar.

Jagoarn ya bayyana ‘jaruntaka da basirar mutane da kuma jin wajibcin sauke nauyin da ke kai kuma a lokacin da ya dace wajen shiga fagen daga' a matsayin tushe na asali na wannan yunkuri na 19 ga watan Dey daga nan sai ya ce: Wannan yunkuri da ke cike da tarihi ya faru ne don kare martabar marigayi Imam Khumaini (r.a), sannan kuma abubuwan da suka biyo baya su ne suka haifar da nasarar juyin juya halin Musulunci.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar a bisa lissafi na abin duniya ana iya cewa nasarar juyin juya halin Musulunci a irin wancan lokacin a gwamnatin kama-karyar take cikin karfinta da kuma samun goyon bayan manyan kasashen duniya ba abu ne mai yiyuwa ba, daga nan sai ya ce: Amma nasarar wannan juyin ya tabbatar da samuwar sunna ta Ubangiji, wato samuwar wasu dokoki da tsare-tsare a wannan duniya wadanda mutanen da suka sa duniya a gaba sun gaza wajen fahimtarsu.

Jagoran ya ci gaba da cewa: A halin yanzu ma dai gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana fada ne sansanonin makiya da suka hada da Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila, ‘yan amshin shatan ma'abota girman kai da masu kafirta mutane da kungiyoyin ta'addanci irin su Da'esh, wanda matukar muka yi aiki da wadannan kayan aiki na tabbatar da Sunnar Ubangiji, wato, tsayin daka, basira da kuma aiki a daidai lokacin da ya dace, to kuwa ko shakka babu za mu yi galaba a kan wadannan sansanonin kamar yadda juyin juya halin Musulunci yayi nasara.

Daga nan sai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya koma ga batun dalilan ci gaba da wanzuwar juyin juya halin Musulunci idan aka kwatanta shi da wasu abubuwan da suka faru cikin tarihin Iran da ma duniya baki daya.

Haka nan yayin da yake ishara da abubuwa guda biyu da suka faru a cikin tarihin na Iran, wato ‘yunkurin ‘yan kasantar da kamfanin man fetur' da kuma ‘yunkurin kundin tsarin mulki', Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: A yayin yunkurin ‘yan kasanci, bukatar mutane wata bukata ce wacce ta ginu bisa son gutsure hannayen turawan Ingila daga albarkatun man fetur na kasar Iran, haka nan a yunkurin kundin tsarin mulki ma bukatar mutane ita ce iyakance irin karfi da iko maras iyaka na sarki Shah.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Duk da cewa wadannan abubuwa guda biyu, duk da cewa suna da wata manufa takaitacciya kuma mutane sun kasance a fage amma sun sha kashi, amma juyin juya halin Musulunci duk kuwa da cewa yana da wata manufa ce guda daya, wato ‘yancin kai da kawo karshen gwamnatin kama karya ta Shah, ya kai ga nasara sannan kuma ya ci gaba da wanzuwa.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Matukar matasa suka yi wa wannan lamari ingantacciyar fahimta, to kuwa kokarin da wasu suke yi na sanya tsoro da yanke kauna cikin zukatan mutane ba zai yi nasara ba, sannan kuma za a tabbatar da ingantacciyar hanyar isa ga kyakkyawar makoma ga kasar nan.

Jagoran yayi ishara da irin kauce wa hanya da juyin juya halin Faransa da Tsohuwar Tarayyar Sobiyeti suka fuskanta da kuma yadda suka sha kashi inda ya ce: Juyin juya halin Musulunci na Iran shi ne kawai juyin juya halin da ya sami damar ci gaba da wanzuwa karkashin asalin koyarwarsa ta farko.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da kokarin da cibiyoyin tunani da tsare-tsare ma'abota girman kan duniya suke yi wajen kawar da abubuwan da suke tabbatar da wanzuwar juyin juya halin Musuluncin, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewar: Dukkanin kokarin makiya tsawon shekarun da suka gabata, ciki kuwa har da kallafaffen yaki, takunkumin tattalin arziki musamman na shekarun baya-bayan nan, manufarsu ita ce kawar da abubuwan da suke tabbatar da wanzuwar wannan juyin ne.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A shekarar 1999 Amurkawa sun yi kokarin aiwatar da abubuwan da suka aiwatar a wasu kasashe kuma suka yi nasara, wato fakewa da batun zabe, sun so su cutar da zaben da aka gudanar ta hanyar amfani da wasu ‘yan tsirarru da suka sha kaye a zaben da kuma ba su goyon baya ta siyasa da kudi. To amma wannan yunkuri na su ya sha kashi a Iran albarkacin tsayin dakan mutane.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin goyon bayan da shugaban Amurka ya ba wa masu adawa da wannan tsari na Musulunci a lokacin rikicin shekarar 1999, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Gwamnatin Amurka ta yi dukkanin abin da za ta iya wajen goyon bayan wadanda suka tayar da wannan rikicin, to amma kasantuwar mutane a fage kuma a lokacin da ya dace, ya mayar da wannan yunkurin ya zamanto aikin baban giwa.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A halin yanzu Amurkawa suna fadin cewa za su kara kaimin takurawa Iran bayan yarjejeniyar nukiliya, kai ka ce kafin wannan lokacin ba su kasance masu takurawa Iran din ba. Amma matasa, mutane da kuma jami'an gwamnati sun tsaya kyam, cikin dogaro da Allah da kuma irin karfin da ake da shi a kasar nan wajen fada da makiyan. Lalle wannan lamari ne mai muhimmancin gaske.

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi magana ne kan zabubbukan da za a gudanar nan gaba a Iran, inda ya ce: Jin wajibcin sauke nauyin da ke wuyan ta hanyar fitowa yayin zabe wani lamari ne da zai hana makiya kai wa ga manufarsu. Hakan kuwa daya ne daga cikin abubuwan da suke tabbatar da wanzuwar juyin juya halin Musulunci.

Ayatullah Khamenei ya bayyana abubuwa guda biyu a matsayin wasu abubuwa masu muhimmanci yayin zabe: Na farko; shi ne asalin fitowa yayin zaben, sannan na biyu kuma shi ne gudanar da zaben yadda ya dace da kuma zaban ‘yan takaran da suka fi dacewa.

Haka nan kuma yayin da yake sake jaddada wajibcin fitowar dukkanin mutanen da suka cancanci kada kuri'a yayin zaben, Jagoran cewa yayi: Kamar yadda na saba fadi, wajibi ne kowa da kowa, hatta wadanda ba su yarda da wannan tsarin ko kuma Jagora ba, su fito kwansu da kwarkwatansu yayin zaben, don kuwa zabe dai kaya ne na al'umma, Iran da kuma tsarin Jamhuriyar Musulunci ne.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewa fitowar dukkanin mutane yayin zabe wani lamari ne da zai tabbatar da karfi da kuma wanzuwar tsarin Musulunci na Iran, tabbatar da tsaro da karin matsayi da mutumcin al'ummar Iran a idon al'ummomin duniya bugu da kari kan kan bada kasa a idanuwan makiya Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Haka nan kuma yayin da yake karin bayani kan muhimmancin da ke tattare da zaban ‘yan takaran da suka fi dacewa, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa yayi: Babu matsala cikin samun mabambantan ra'ayi, abin da ke da muhimmanci shi ne mu yi taka tsantsan da sanya ido wajen ganin zaben da za mu yi ya zamanto zabe ne ingantacce.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Matukar aka yi hakan, to ko da kuwa wasu daga cikin wadanda aka zaban ba su dace ba, to kuwa kokarin da masu zaben suka yi wajen zaben dan takaran da ya dace, zai zamanto abin yardar Ubangiji Madaukakin Sarki.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da matsayi mai girma da majalisar shawarar Musulunci ta ke da shi a cikin lamurra na cikin gida da kuma na kasa da kasa, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Majalisa tana da muhimmanci maras tamka a bangarori daban-daban musamman a bangaren kafa dokoki da kuma share fagen ci gaban gwamnati da kuma tsayin dakan al'umma.

Jagoran ya bayyana matsayar da majalisar ta dauka a fagage na kasa da kasa a matsayin matsaya mai kyau inda ya ce: Akwai bambanci tamkar sama da kasa tsakanin majalisar da ta yi tsayin daka a gaban makiya cikin lamurran nukiliya da sauran lamurra, ta tsaya kyam cikin jarunta da ‘yanci wajen bayyanar da matsayar al'umma, da majalisar da take maimaita maganganun makiya cikin lamurra daban-daban.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar kowane guda daga cikin ‘yan majalisar yana da rawar da zai taka cikin matsayar da ake dauka a majalisar don haka sai ya ce: A saboda haka ne wajibi ne mutanen dukkanin jihohi da garuruwa su sanya ido sosai yayin zaben wakilansu da kuma yin zaben da ya dace.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Tabbas fahimtar daidaikun ‘yan takara ba karamin aiki ba ne, to amma za a iya sanya ido kan tarihi da matsayar mutanen da suka gabatar da jerin sunayen ‘yan takaran zaben, sai a yanke shawara da daukan matsaya kan jerin sunayen.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Idan har wadanda suka gabatar da jerin sunayen ‘yan takaran sun zamanto muminai ne masu riko da juyin juya halin Musulunci, sannan kuma sun yi amanna da tafarkin marigayi Imam Khumaini, to ana iya yarda da jerin sunayen ‘yan takaran da suka gabatar don zaben majalisar shawarar Musulunci da kuma majalisar kwararru ta jagoranci. To amma idan har bas a ba wa juyin juya hali da addini da ‘yancin kasa wani muhimmanci na azo a gani sannan kuma zukatansu suna son tabbatar da maganganun Amurka da sauran ma'abota girman kai ne, to lalle ba abin yarda ba ne.

Ayatullah Khamenei ya bayyana majalisar kwararru ta jagoranci a matsayin wata majalisa mai matukar muhimmanci inda ya ce: Sabanin wasu tunanin, ba wai an kirkiri majalisar kwararru don taro sau daya ko sau biyu a shekara da gabatar da jawabai ba ne, face dai aikinsu aikinsu shi ne zaban jagora, wanda ja-gaban wannan yunkuri na juyi a duk lokacin da jagora mai ci ya bar duniya. Wannan batu ne mai matukar muhimmanci.

Haka nan yayin da yake magana kan wajibcin sanya ido sosai wajen zaben ‘yan takaran majalisar kwararru, Jagoran ya bayyana cewar: Bisa la'akari da yanayin majalisar kwararru mai yiyuwa ne a yayin bukata su zabi wani jagora wanda ta hanyar dogaro da Allah cikin jaruntaka ya tsaya kyam wajen tinkarar makiya da kuma ci gaba da riko da tafarkin marigayi Imam Khumaini. Amma kuma akwai yiyuwar su zabi wani mutum wanda ba shi da irin wadannan siffofi. A saboda haka wajibi ne a zabi ‘yan wannan majalisar bayan bincike da sanya ido da kuma masaniya.

Ayatullah Khamenei ya bayyana fitowar mutane yayin zabe musamman yin taka tsantsan wajen zaben dan takaran da ya dace wani lamari ne zai kai ga cimma wasu manufofi guda biyu masu muhimmanci: su ne kuwa ci gaba da wanzuwar juyin juya halin Musulunci da kuma tabbatar da zaman lafiya da kuma kwanciyar hankalin al'umma.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: A halin yanzu ma matukar mutane suka yi aki da nauyin da ke wuyansu wajen zaben ‘yan takaran da suka dace a majalisun shawarar Musulunci da ta kwararru, to kuwa ci gaban juyin juya halin Musulunci zai ci gaba da karuwa sannan kuma za a tabbatar da ci gaban wanzuwar juyin.

Ayatullah Khamenei ya kawo wasu ayoyi na Alkur'ani da suke nuni da sauka sakina da kwanciyar hankali ga zukatan muminan da suka yi mubaya'a ga Ma'aikin Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, inda ya ce: A yau ma duk wanda yayi mubaya'a wa juyin juya halin Musulunci da kuma marigayi Imam Khumaini (r.a) da kuma tafarkinsa, to hakan yana a matsayin mubaya'a ce ga Annabi (s.a.w.a), sannan kuma Allah Madaukakin Sarki zai fitar da damuwa da rashin kwanciyar hankali daga zukatan mutane da mayar da su da kwanciyar hankali da yarda a matsayin ladar wannan mubaya'a da suka yi.

Daga karshen Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Ko shakka babu ci gaban wanzuwar juyin juya hali, tsayin daka cike da fata da kwanciyar hankalin al'umma lamurra ne da za su tabbatar da nasarar al'umma a kan Amurka da kuma makirce-makircen makiya.


http://iqna.ir/fa/news/3465718

captcha