IQNA

An Samu Wani Kur’ani Lafiya Lau A wani Gida Da Gobara Ta Kona A Ghana

15:59 - January 10, 2016
Lambar Labari: 3480036
Bangaren kasa da kasa, an samu wani kwafin kur’ani mai tsarki a cikin wani gida da gobara ta kama a kasar Ghana kuma ta kona komai a cikin gidan in banda kwafin kur’anin.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gioz na Ghanaweb cewa, gobarar ta tashi ne a wani gida da ke garin Skondi da ke kasar ta Ghana da ke yammacin Afirka.

Bayanin ya ce wasu mutane ne daya dan kasar ta Ghana da kuma wasu yan kasar Lebanon su 2 suke zaune a cikin gidan, amma a lokacin da abin ya faru babu kowa a cikin gidan.

Bayan da wutar ta mutu sakamakon kasha ta da aka yi, an samu cewa dukaknin kayan da suke cikin gidan sun kone baki daya, amma kuma abin mamaki shi ne an samu wani kwafin kur’ani mai tsarki wuta bata taba shi ba.

Wannan dai bas hi ne karon far4ko da ake samun bayani kan cewa wuta taci wurare ba, amma kuma a samu kwafin kur’ani lafiya lau ba tare da ya kone ba.

http://iqna.ir/fa/news/3466129


captcha