Bangaren siyasa, a lokacin da yake ganawa da manyan jami’an hukumar zabe ta kasa jagoran juyin juya hali ya bayyana cewa wajibi ne a kiyaye kaidoji da dokokin zabe a lokacin zabuka, kamar yadda ya jinjinawa masu shiga tattaunawa na kasar kan yarjejeniyar nulkiliya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jagora cewa, A safiyar yau Laraba ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Ozma Sayyid Ali Khamenei ya gana da jami'ai da masu gudanar da zaben majalisar shawarar Musulunci ta Iran kawo na goma da kuma zabe na biyar na majalisar kwararru ta jagoranci inda yayi karin haske dangane da ma'anar ingantacce kuma lafiyayyen zabe, kamar yadda kuma yayi karin haske da ishara da wasu batutuwa masu muhimmanci da suka shafi fara gudanar da yarjejeniyar nukiliya da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya inda ya kirayi jami'an kasar da cewa:, Amurka dai ita ce dai wancan tsohuwar Amurkan, ba ta sauya ba, don haka wajibi ne a yi taka tsantsan dangane da yaudararta yayin aiwatar da abubuwan da aka cimma a yarjejeniyar nukiliyan.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana wadannan zabubbuka guda biyu da za a gudanar da su a nan gaba a Iran a matsayin wasu lamurra masu muhimmancin gaske, yana mai bayyana zaben a matsayin wata gasa ta kasa inda ya ce: A yayin wannan gasar, a wajen al'umma babu wani wanda yayi nasara ko kuma wanda ya sha kashi, don kuwa a dukkanin yanayi biyu, al'ummar Iran su ne wadanda suka yi nasara.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Matukar al'ummar Iran suka shiga fagen zabe da dukkan karfi da kuma azamarsu, sannan suka cika akwatunan zabe da kuri'unsu, to kuwa Jamhuriyar Musulunci za ta samu daukaka da kuma zama abin alfahari.
Daga nan sai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya shiga fagen bayanin abubuwan da suke tabbatar da lafiyayyen gasa yayin zabe inda ya ce: Mafi muhimmancin sharadin ingantacciyar gaza, shi ne fitowar dukkanin wadanda suka cancanci kada kuri'a su kuma kada kuri'arsu, hatta mutanen da suke da matsala da wannan tsarin.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Mai yiyuwa ne wasu su zamanto suna da matsala da wannan tsarin, to amma a mafi yawan lokuta irin wadannan mutanen ba su da matsalada tsaro, ci gaba da kuma daukakar kasar nan. A saboda haka idan har suna son tabbatar tsaron kasa, karuwar daukaka ta kasa da kuma tabbatar da ci gabanta, to wajibi ne su fito su kada kuri'unsu yayin zaben.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Koda yake mutanen da suka fito zaben don sauke nauyin da ke wuyansu da kuma tsarkakakkiyar niyya, ko shakka babu za su janyo fagen samun yardar Allah ga kawukansu.
Don haka sai Jagoran ya ce: Sharadi na fako kuma mai muhimmanci na tabbatar da lafiyayyiyar takarar zabe, shi ne fitowar al'umma kwansu da kwarkwatansu yayin zabe. Kuma da yardar Allah, haka al'ummar Iran ma'abota basira za su fito yayin wadannan zabubbuka guda biyu.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Wasu suna nan sun dana tarko don cutar da tsarin Jamhuriyar Musulunci ta hanyar kashe gwiwan mutane wajen kar su fito zabe ko kuma raunana tushen zaben. To amma al'ummar Iran sun kawar da wannan taron, kuma a wannan zaben ma za su yi hakan.
Jagoran ya bayyana fitowa fitowa zabe cikin basira da kuma zaben mutanen da suka dace a matsayin sharadi na biyu na lafiyayyen zaben, daga nan sai ya ce: Ku zabi mutanen da bayan sun zauna a kujerar shugabancin, za su zamanto masu damuwa da matsalolin da kasa take ciki da kuma gabatar da kansu a matsayin masu hidima ga manufofin al'umma, sannan kuma ba za su sayar da kasar nan ga makiya kamar yadda kuma ba za su sanya kafafunsu su take manufofi da amfani na kasa ba.
Har ila yau kuma yayin da yake ishara da maganar da yayi a baya na cewa ‘ya kamata hatta mutanen da suke da matsala da wannan tsarin su fito yayin zaben', Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Wannan maganar ba tana nufin ku zabi mutumin da bai yi imani da wannan tsarin, ku tura shi zuwa majalisa ba ne.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Babu wani waje a duniyan nan da ake barin mutanen da ba su yi imani da tsarin wannan kasar su rike mukamai a cibiyoyin masu tsara siyasar kasar ba, hatta a kasashe irin su Amurka da suke kiran kansu a matsayin masu kare ‘yancin mutane, sannan wasu masu karamin tunani kuma suka yarda da hakan. A lokacin yakin cacar baki tsakanin kasashen gabashi da yammaci, komai kashin zargin da ake yi wa mutum da riko da tsarin gurguzu, nan take za a yi waje da shi.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Fadin da muke yi cewa wajibi ne mutanen da za a tura su zuwa majalisar su zamanto masu amanna da tsarin da kuma kiyaye manufofinsa, hakan wani hakki ne na al'umma wanda yake da tasiri cikin ingancin zabe.
A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi karin haske kan wasu bangarori na lafiyayyen zaben inda ya ce: "kiyaye doka a tsakanin dukkanin cibiyoyin da alhakin gudanar da zabe yake wuyansu', "nesantar cin mutumcin juna a tsakanin ‘yan takara kai hatta ma cin naman juna", "nesantar alkawurran da a aikace ba za a iya aiwatar da su ba ko kuma wadanda suka saba wa doka" da kuma "mu'amala ta gaskiya da mutane" suna daga cikin wasu siffofi da dabi'u na lafiyayyen takarar zabe.
Yayin da yake magana kan kokarin wasa da kwakwalan mutane, Ayatullah Khamenei yayi ishara da wasu dabi'u da ma'amaloli marasa kyau, daga nan sai ya ce: Wasu mutane a koda yaushe suna ci gaba da nanata kalmar ‘masu ra'ayin rikau' wanda abin nufinsu shi ne kungiyoyi mutane ma'abota imani da riko da tafarki juyin juya hali. Alhali kuwa bai dace a dinga tuhumar matasa masu riko da koyarwar juyin juya halin Musulunci da tsaurin ra'ayin rikau ba. Don kuwa wadannan matasan sun kasane a fage da dukkanin karfi da kuma kyakkyawan niyya. A duk lokacin da ba da kariya ga kasar nan da kuma mutumcinta ya taso, suna nan a sahun gaba.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Bai kamata saboda faruwar wani abu mara kyau kuma babban kuskure kamar hari kan ofishin jakadancin Saudiyya, shi kenan sai a shigo da matasa muminai masu riko da juyin juya hali cikin lamarin da ci gaba da tuhumarsu ba
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Hankali da fahimtar wadannan matasan masu riko da koyarwar wannan juyi da kuma fahimta da yadda suke kallon lamurra a lokuta da dama sun dara irin na wasu manyan mutanen kyau. A saboda haka bai kamata a raunana wadannan matasan ta hanyar fakewa da batun kai hari ofishin jakadancin Saudiyya ko kuma kafin nan ofishin jakadancin Ingila, wadanda dukkaninsu biyu wani lamari ne da ya cutar da kasar nan, da kuma ci gaba da zargi da sukarsu ba.
A karshen maganarsa kan batun zaben, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: zabe dai wata ni'ima ce sannan kuma wata dama ce mai girma, wanda gode wa wannan ni'imar ita ce gudanar da ingantaccen zabe. A saboda haka bai kamata a bari a dushe wannan haske ta hanyar wasu maganganu da dabi'un da ba su dace ba.
A bangare na biyu na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi magana ne da kuma ishara da wasu batutuwa masu muhimmanci kan abin da ya shafi fara aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya kan shirin nukiliyan kasar. Yayin da yake mika godiyarsa dangane da kokarin da shugaban kasar Iran, ministan harkokin waje da sauran membobin tawagar Iran a wajen tattaunawar, Jagoran cewa yayi: Duk da cewa ba dukkanin bukatun Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne aka samu ba, to amma a hakikanin gaskiya jami'an gwamnati sun yi kokari ainun, wanda insha Allahu ladarsu na wajen Allah.
Haka nan kuma yayin da yake sukar mutanen da suke fadin cewa abin da aka samu na sakamakon wannan tattaunawar wani bangare ne na irin tausayi da kuma kyautatawar Amurka, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Wadansu mutane suna son amfani da wannan damar wajen rufe bakar fuskatar ma'abota girman kai, wanda hakan wani abu ne mai muni da kuma hatsarin gaske.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Idan wani dan fashi ya zo ya kwace maka gida da kuma dukiyarka, to amma sai daga baya bayan kokari da wahalhalu ka sami nasarar korarsa daga wani bangare na gidan naka. To shin wannan sakamako ne na tausayi da kyautatawar wannan dan fashi mai son amfani da karfin, ko kuma sakamako ne na karfi da kuma kokarinka?
Ayatullah Khamenei ya jaddada cewar: Nasarar da aka samu a fagen nukiliya, ta samu ne albarkacin kokarin masanan Iran, ciki kuwa har da shahidan nukiliyan su hudu masu girma bugu da kari kan goyon baya da tsayin dakan al'umma, sannan da kuma kokarin jami'an gwamnati wanda hakan ne ya tilasta wa makiya ja da baya a wasu bangarorin. A saboda haka babban rashin adalci ne wasu su bayyana hakan a matsayin wani tausayi da kuma kyautatawar Amurkan.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da maganganun baya-bayan nan da wasu jami'an Amurka suka yi, Jagoran ya bayyana cewar: Manufar makiya wajen sanya wadannan takunkumin, ita ce tunzura mutane da sanya su fitowa kan tituna don nuna rashin amincewarsu. To amma mutane sun tsaya kyam, sannan tare da jami'an gwamnati sun tabbatar da daukaka da mutumcin kasar nan.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Koda yake na yi amanna da cewa ana iya yin sama da haka, to amma ala kulli hal kokari da damar da ake da ita ita ce ta haifar da wannan sakamakon wanda shi din ma wani aiki ne mai kyau kana kuma mai muhimmanci abin jinjinawa.
Ayatullah Khamenei ya bayyana Amurka a matsayin ‘babbar gunki' sannan sauran masu son amfani da karfi a kan sauran kasashe kuma a matsayin ‘yan amshin shatan ma'aboita girman kan. Har ila yau kuma yayin da yake karin haske hakikanin manufar makiyan Iran dangane da wannan batu na nukiliya, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa yayi: Lalle ana iya rantsewa da cewa masu kiyayya da mu sun san cewa ba ma da nufin kera makaman nukiliya, to amma suna da wata manufar ce ta daban.
Jagoran ya bayyana dakatar da yunkurin ci gaba na al'ummar Iran da kawo karshen irin tasirin da Iran take ci gaba da samu a yankin nan da kuma duniya a matsayin babbar manufar ma'abota girman kai wajen kara tsananta matsin lambar da suke a kan batun nukiliyan. Daga nan sai ya ce: Wadannan mutane suna so ne su yi amfani da wannan hanyar wajen sanyawa al'ummar Iran cewa Jamhuriyar Musulunci ta gaza wajen gina wani tsari wanda ya ginu bisa koyarwar addini.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Wajibi ne kowa da kowa ciki kuwa har da jami'an gwamnati su fahimci wannan babbar manufa ta Amurkawan. Suna so ne ta hanyar amfani da tursasawa da kuma farfaganda su cimma manufarsu. A saboda haka wajibi ne a yi taka tsantsan da kuma nuna hangaen nesa wajen fada da hakan.
Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi jami'an gwamnati da ‘yan kwamitin sanya ido kan yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma da su yi taka tsantsan da yaudarar Amurka yana mai cewa: Daya bangaren da ke fuskantarmu, mayaudari ne. Don haka kada ku dogara da kuma yarda da dariya da sakin fuskarsa.
Jagoran ya bayyana cewar manufar Amurka dai ita ce dai wancan manufar ta su ta nuna adawa da kiyayya da al'ummar Iran irin na lokacin Reagan da Bush, babu wani sauyi cikin haka don haka sai ya ce: Wajibi ne jami'ai su yi taka tsantsan da sanya ido wajen ganin lalle Amurkawa sun yi aiki da nauyin da ke wuyansu. Idan kuwa ba haka ba, to wajibi ne a rama wa kura aniyarta.
Har ila yau kuma yayin da yake jinjinawa da kuma godewa yunkurin da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran suka yi na kame sojojin kasar Amurka a lokacin da suke shigo cikin ruwan kasar Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Lalle wadannan mutanen sun tabbatar da karfi da daukakar Iran a lokacin da makiya suka ketare iyaka. A saboda haka wajibi ne jami'an gwamnati su ma su aikata irin haka a dukkanin fagage. A duk inda makiya suka ketare kan iyakan manufofin kasar Iran, to su tinkari hakan da dukkan karfinsu.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da wata dabi'ar ta daban ta Amurka, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Abubuwan da ke faruwa a halin yanzu a yankin nan suna nuni da tsohuwar manufar da Amurka take da ita na wajibcin kafa wani sabon yankin Gabas ta t sakiya. Wato sabon Gabas ta tsakiya a wajensu, shi ne gabas ta tsakiyan da ke cike da yaki, ayyukan ta'addanci da rikice rikice na mazhaba da basasa da kuma koma baya. Don haka sai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi dukkanin al'umma da cewa: Wajibi ne a fahimci irin wadannan ayyuka na Amurkasosai.
Daga karshe dai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar dage takunkumin da aka yi wa Iran ba shi ne kawai abin da zai magance matsalolin da kasar take fuskanta ba, yana mai kiran jami'an kasar da su zage damtse wajen aiki tukuru wajen magance matsalolin da ake fuskanta musamman a fagen tattalin arzikin.
Kafin jawabin Jagoran sai da Ayatullah Ahmad Jannati, babban sakataren majalisar kula da kundin tsarin mulki na Iran da kuma ministan cikin gida na kasar Malam Rahamani Fadhli suka gabatar da jawabansu kan irin ayyukan da suka gudanar wajen ganin an gudanar da lafiyayyen zabe a kasar ta Iran.