IQNA

Wata Tsohuwa Ta Hardace Kur’ani Mai Tsarki A UAE

22:06 - January 25, 2016
Lambar Labari: 3480075
Bangaren kasa da kasa, wata tsohuwa ‘yar shekaru 82 a kasar hadaddiyar daular larabawa ta hardace juzui 10 na kur’ani mai tsarki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na KTimes cewa, Shaikhah Zaen Sa’d Suraidi daga yankin Uzun na Ra’asul Khaimah yar shekaru 82 ta hardace wani bangare na kur’ani.

Wannan tsohuwa ta bayyana cewa ita ba ta iya karatu da rubutu ba, amma kuma ta sanya kanta ganin cewa ta yi ta sauraren karatun kur’ani mai tsarki.

Ummu Muhammad a ce naurorin zamani da ake saka sautin kur’ani yana karantawa yana maimaitawa ya taimaka mata matuka, inda takan saurara ta yi ta maimatawa.

Ta ce a halin yazu ta hardace kusan kashi daya bisa uku na kur’ani mai tsarki ta wannan hanya, kuma za ta ci gaba da yin hakan, domin ganin ta kara samun rabo na daga hardar kur’ani.

Haka nan kuma ta kara da cewa a shirye take ta shiga gasar hardar kur’ani mai tsarki da za agudanar nan ba da jimawa ba ta kasar hadaddiyar daular larabawa.

3470083

captcha