IQNA

Mufti Na Kasar Masar:

Addinin Muslunci Yana Kare Dukkanin Bil Aadama Ne

22:55 - January 26, 2016
Lambar Labari: 3480079
Bangaren kasa da kasa, Shauki Allam babban mai bayar da fatawa akasar Masar ya bayyana cewa addinin muslunci yana kare dukkanin yan adam ne baki daya da suke rayuwa abayan kasa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwafd cewa, Shauki Allam babban mufti na kasar Masar ya bayyana cewa addinin muslunci yana kare hakkokin dukkanin yan adam ne, domin kuwa a kowane lokaci muslunci yana kallon mutum ne a matsayinsa na dan adam  a matakin farko.

Ya ci gaba da cewa babu ta’assubanci a cikin addinin muslunci, a kowane lokaci musulunci yana nan kan matsayinsa na girmama dan adam da mahangarsa da kuma kiyaye hakkokinsa.

Kamar yadda ya yi ishara da cewa muslunci yana kallon mutum  a matsayin bil adama, wanda yake da hakkoki na musamman, kuma koda baya yana kan akida ta muslunci ba ne, dole ne a kiyaye hakkokinsa da kare lafiyarsa, kamar yadda hakan yake a cikin koyarwar wannan addini mai girma.

Ya kara da cewa wadanda ba musulmi ba ne da suke rayuwa a kasashen musulmi sheda ne kan hakan, domin kuwa ana kiyaye hakkokinsu ba tare da cutar da sub a.

Majdi Ashur daya daga cikin wadanda suke halartar taron a maroko inda aka gabatar da wannan jawabi, shi ma daga kasar ta Masar ya bayyana cewa, wadanda suke rayuwa  akasar Masar sun san yadda wadanda ba musulmi ba suke rayuwa a cikin yancinsu.

Wannan taro na kasa da kasa an fara gdanar da shi ne a jiya, domin tattauna hanyoyin ci gaba da kare hakkokin marassa rinjaye a cikin kasashen musulmi.

3470493

 

captcha