Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wata gasa domin zabar wadanda za su wakilci kasar Mauritaniya a gasar kur'ani mai tsarki ta duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na arabstoday cewa, an fara gudanar da gasar kur'ani ta tajwidi ne a halin yanzu a masallacin madinatu munawwara a birnin Nuwakshot, domin tantance wadanda suka cancanci wakiltar kasar a gasar kur'ani ta kasa da kasa a tsakanin mutane 269 masu karawa da juna.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan yana daga cikin shirin da ma'aikatar kula da harkokin addinin muslunci take da shin a karfafa ayyukan kur'ani da kuma halartar gasa.
Sayyid Ahmad Wuld Ahlu Dawud ne ya jagoranci bude gasar, inda za a samu kwanaki goma a nan gudanar da ita, kafin daga karshe a tantance.
Ya ce yana fatan masu gasar za su maida himma domin samun matsayin da zai ba damar hakartar gasar kasa da kasa.
Sayyid Ahmad Wuld Ahlu Dawud ya ce gwamnatin kasar ta taka bababr rawa domin ganin cewa wanann shiri ya cimma nasara kamar yadda aka shirya shi.
Muhammadul Amin Wuld Sheikhuna wuld sheikh Ahmad shugaban bangaren kula da harkokin kur'ani a ma'akatar kula da ayyukan addini ya bayyana cewa, wanann shiri yana da matukar muhimamnci, kuma da yardarm ubangiji za a ci gaba da gudanar da shi.
Ya kara da cewa wasu daga cikin kwarrau kan harkokin kur'ani ne za su dauki nauyin kula da wannan lamari, tare da karfafa gwaiwar matasa da wadanda suka nuna kwazo domin tabbatar da nasar lamarin.