IQNA

An Gudanar Da Gasar Hardar Kur’ani A Ethiopia

19:42 - February 12, 2016
Lambar Labari: 3480130
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wata gasar hardar kur’ani mai tsarki tare da halartar mutane 111 a kasar Ethiopia da suka hada maza da mata.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hqmi.org cewa, an gudanar da wannan shiri ne na gasa tare da hadin tsakanin cibiyar kula da ayyukan hardar kur’ani da Habasha da kuma ta kasa da kasa.

An gudanar da wannan gasa ne a cibiyar muslunci ta Annur da ke yankin Didawa a gabashin kasar ta Eythiopia, inda alkalai suka sanya ido kan bangarorin gasar, wanda ya hada hardar dukkanin kur’ani mai tsarki, da kuma izihi 20, sai kuma izihi 10, da kuma 5.

An samu halartar manyan mutane a lokacin bayar da kyautuka ga wadanda suka nuna kwazo, da suka hada da sheikh Umar Khidair Ambur, shugaban majalisar musulmin yankin Dir Dawa, sai kuma Sheikh Abdulsalam Umar, mataimakin shugaban cibiyar Annur, da kuma Khalid Bin Usman wakilin cibiyar hardar kur’ani ta duniya.

An dai gabar da bayanai ga wadanda suka samu halartar wannan gasa, bayanan dai sun mayar da hankali kan muhimamncin yin aiki dsa koyarwar kur’ani, maimakon takata da karatunsa kawai ba tare da yin la’akari da darussan da ke cikinsa.

Daga karshe dai an bayar da kyautuka ga wadanda suka nuna kwazo a wannan gasa.

Kasar Ethiopia dai na da sunan jamhuriyar dimokradiyya ta Fedraliyyar Ethiopia, tana gabacin Afirka ne, kuma tana mutane kimanin miliyan 82.5, da kuma kilo mita miliyan 1/100 wadda it ace kasa ta goma wajen fadi a Afirka.

3474953

captcha